Wednesday, 23 August 2017

*FITOWA TA 6
*Daga Littafin:-SUFANCI DA AKIDUN SUFAYE.
*Jerin Littafan Sufanci Na 1.
Wallafar:-Prof.Umar Labdo(hafizahullah)
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com

Saboda haka,domin amfanin makaranta wadanda suke baki ne su a
wannan fage,sai mu ce a takaice Sufanci wani tafarki ne wanda masu
ibada suke bi don neman cimma yardar Ubangiji.Kashin bayan Wannan
hanya shi ne hakuri da rayuwar talauci,da nesantar dukkan abubuwan jin
dadi na rayuwa,da tsarkake zuciya da daukakar rayi.Sufi kuwa shi ne
duk mutumin da yake bin wannan tafarki.
Mai karatu zai lura da bambanci tsakanin Sufanci kamar yadda
sufaye magabata suka siffanta shi da yadda yake a yau.Alal
misali,batun hakuri da rayuwar talauci da nesantar jin dadi da
tsarkake zuciya da gudun duniya,sufayen zamaninmu ba su San su ba.Yau
abinda Sufanci yake nufi shi ne a ci a sha a yi maya-maya,a yi wada da
wadaka,kuma a tara abin duniya.Wannan ya sa da sufaye da Sanatoci a
yau da wuya mutum yake iya rabe su a tufafinsu da motocinsu da manyan
gidajensu.Haka nan ya'yansu da matayensu.

Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 7 Insha Allah
Abu Aisha journalist
Jibwis Social Media Katsina

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve