Monday, 28 August 2017

HUKUNCIN ASKI DA YANKE FARCE GA MAI LAYYAH A MAZHABAR MALIKIYYA

HUKUNCIN ASKI DA YANKE FARCE GA MAI LAYYAH A MAZHABAR MALIKIYYA

Hadisi ya tabbata daga Annabi (saw) cewa; idan watan Zul Hijja ya kama to duk wanda yake da niyyar layyah kar ya yi aski, kar ya yanke farce har sai ya yanka layyarsa.

Malaman Mazhabar Malikiyya sun yi aiki da wannan Hadisi saboda Sahabbai sun yi aiki da shi kamar yadda Imamuna Malik ya ruwaito a cikin Mawatta:
حدثني يحيى، عن مالك، عن نافع، أن عبد الله بن عمر «ضحى مرة بالمدينة» - قال نافع «فأمرني أن أشتري له كبشا فحيلا أقرن، ثم أذبحه يوم الأضحى في مصلى الناس» قال نافع: ففعلت. ثم حمل إلى عبد الله بن عمر «فحلق رأسه حين ذبح الكبش، وكان مريضا لم يشهد العيد مع الناس».
قال نافع وكان عبد الله بن عمر يقول: «ليس حلاق الرأس بواجب على من ضحى»، وقد فعله ابن عمر.
موطأ مالك ت عبد الباقي (2/ 483)

"Yahya ya ruwaito daga Malik, daga Nafi'u ya ce: Lallai wani lokaci Abdullahi dan Umar (ra) ya yi layyah a Madina, sai ya umurce ni na saya masa rago namiji mai kaho, sa'annan na yanka shi ranar Layyah a Masallacin Eidi.
Nafi'u ya ce: sai na yi hakan, sai aka dauki yankakken ragon aka kai wa Abdullahi dan Umar (ra), sai ya aske kansa bayan an yanka ragon, ya kasance ba shi da lafiya bai halarci Sallar Eidi da mutane ba.
Nafi'u ya ce: Abdullahi dan Umar (ra) yana cewa: "Aske kan ba wajibi ba ne a kan wanda ya yi layyah". Amma shi Abdullahi dan Umar (ra) ya aikata hakan.

Malaman Malikiyya sun yi sharhin wannan "Athari" na Ibnu Umar (ra) kamar haka:
1- Abul Waleed Albajiy ya ce:
ولعله كان امتنع من حلق رأسه وشيء من شعره من أول العشرة حين أراد أن يضحي على وجه الاستحباب وإن لم ير ذلك واجبا على ما ذكر في آخر الحديث.
وقد روى الشيخ أبو بكر والقاضي أبو الحسن أنه يستحب لمن أراد أن يضحي إذا رأى هلال ذي الحجة أن لا يقص من شعره ولا يقلم أظفاره حتى يضحي قالا: ولا يحرم ذلك عليه...
والدليل على استحباب ذلك ما رواه أبو عبد الرحمن حدثنا سليمان بن مسلم البلخي ثقة وسليمان بن مسلم الحضاري ليس بثقة حمصي أخبرنا البصري أخبرنا شعبة عن مالك عن ابن مسلم عن سعيد بن المسيب عن أم سلمة عن النبي - صلى الله عليه وسلم - قال: «من رأى هلال ذي الحجة فأراد أن يضحي فلا يأخذن من شعره ولا من أظفاره حتى يضحي» قال أبو عبد الرحمن عمر بن مسلم بن عمار بن أكيمة: قد اختلف في اسمه فقيل عمرو وقيل عمر وهو مدني.
فوجه الدليل منه إن هذا نهي والنهي إذا لم يقتض التحريم حمل على الكراهية ودليلنا على نفي الوجوب حديث عائشة المتقدم في كتاب الحج «أنا فتلت قلائد هدي رسول الله - صلى الله عليه وسلم - بيدي ثم بعث به مع أبي فلم يحرم على رسول الله - صلى الله عليه وسلم - شيء أحله الله له حتى نحر الهدي» ولا خلاف أن النبي - صلى الله عليه وسلم - ضحى في ذلك العام.
المنتقى شرح الموطإ (3/ 90 - 91)

"Ta yiwu Abdullahi dan Umar (ra) ya ki aske kansa da sauran gashin jikinsa ne tun daga farkon kwanaki goma na Zul Hijja, lokacin da ya yi niyyar yin layyah a bisa matsayin MUSTAHABBANCI, duk da cewa; bai dauki hakan a matsayin wajibci ba, bisa yadda aka ambata a karshen Hadisin (Atharin).
Hakika Shaikh Abubakar (Al- Abhariy 375 هـ) da Alkali Abul Hassan (Ibnul Qassar 397 هـ) sun ruwaito cewa; MUSTAHABBI ne ga wanda yake da nufin yin layyah idan ya ga jinjirin watan Zul Hijjah kar ya aske gashinsa, kar ya yanke farcensa har sai ya yanka Layyarsa. Suka ce: amma ba haramun ba ne a kansa…
Dalili a kan MUSTAHABBANCIN hakan (shi ne Hadisin Ummu Salamah (ra), wanda Imamu Muslim ya ruwaito).

Fiskar dalili daga Hadisin shi ne; Hadisin hani yake yi a kan aski da yanke farce, hani kuwa idan bai hukunta haramci ba to ana daukansa ne a kan karhanci, dalilinmu a kan kore wajabci shi ne Hadisin A'isha (ra), wanda ya gabata a "Kitabul Hajji"….", Alhali babu sabani cewa; Annabi (saw) ya yi layyah a wannar shekarar".

• Abin lura, Malaman Malikiyya sun ce: hanin da yake cikin Hadisin Ummu Salama (ra) na KARHANCI ne ba na Haramci ba, don haka kin yin aski da yanke farce a cikin kwanaki goman MUSTAHABBI ne saboda Hadisin Ummu Salama (ra), ba haramun ba saboda Hadisin A'isha (ra), shi ya sa Ibnu Umar (ra) ya ki yin aski sai bayan yanka layyarsa.

2- Alkali Ibnul Arabiy:
قوله: "وحلق ابن عمر رأسه حين ذبح الكبش" ولعله امتنع من ذلك حتى ضحى، على وجه الاستحباب، ولم ير ذلك واجبا عليه.
وقد روى الأبهري وابن القصار أنه يستحب لمن أراد أن يضحي ألا يقص ولا يقلم ظفرا حتى يضحي. قالا: ولا يحرم ذلك عليه.....
ودليل الاستحباب: ما روي عن النبي - صلى الله عليه وسلم - أنه قال: "من رأى هلال ذي الحجة، فأراد أن يضحي، فلا يأخذن من شعره ولا من أظفاره حتى يضحي" فوجه الدليل: أن هذا نهي، والنهي إذا لم يقتض التحريم حمل على الكراهية.
ودليلنا على نفي الوجوب: حديث عائشة في كتاب الحج "فلم يحرم على رسول الله - صلى الله عليه وسلم - شيء أحله الله حتى نحر الهدي" ولا خلاف أن النبى - صلى الله عليه وسلم - ضحى في ذلك العام.
المسالك في شرح موطأ مالك (5/ 179 - 180)

Wannar magana irin wacce ta gabata ce daga Al- Bajiy.

3- Al- Maziriy ya ce:
مذهبنا أن الحديث لا يلزم العمل به واحتج أصحابنا بقول عائشة -رضي الله عنها- كان النبي - صلى الله عليه وسلم - يهدي من المدينة فأفتل قلائد هديه ثم لا يجتنب شيئا مما يجتنب المحرم وظاهر هذا الإطلاق أنه لا يحرم تقليم الأظفار ولا قص الشعر، ومذهب ربيعة وأحمد وإسحاق وابن المسيب المنع أخذا بالحديث المتقدم ويرون أن النص على ما ذكر فيه أولى من التمسك بالإطلاق الذي وقع من لفظ عائشة -رضي الله عنها- ومذهب الشافعي حمله على الندب وحكي عن مالك، ورخص فيه أصحاب الرأي.
المعلم بفوائد مسلم (3/ 99)

"Mazhabarmu (ta Malikiyya) lallai ba wajibi ba ne yin aiki da Hadisin Ummu Salamah (ra), Malaman Mazhabarmu sun kafa hujja da Hadisin A'isha (ra): Annabi (saw) yana aika Hadaya Makka amma ba ya nisanta komai daga cikin abin da mai haraman aikin Hajji yake nisanta.
Zahirin wannan Hadisi Mutlaqi (wanda ya zo a sake) ba ya haramta yanke farce da yin aski.
Mazhabar Rabi'ah, Ahmad, Ishaq da Ibnul Musayyab ita ce hani a kan aikata su, riko da Hadisin Ummu Salamah (ra) wanda ya gabata, suna ganin cewa; Nassin Hadisin (na hana yin aski da yanke farce) a bisa yadda aka ambace shi, shi ya fi cancanta a yi riko da shi fiye da riko da Hadisi Mutlaqi (wanda ya zo a sake, ba Nassi ba) wanda ya zo a lafazin A'isha (ra).
Amma Mazhabar Shafi'iy ita ce daukan Hadisin Ummu Salama (ra) a matsayin MUSTAHABBI, KUMA AN HAKAITO HAKAN DAGA MALIK, Mabiya ra'ayi (wadanda ba sa bin Hadisi, 'Yan Hanafiyya) su kuma su sassauta (sun ce: mai layyah ya yi aski ya yanke farce kawai)".

4- Alkali Iyadh kuwa dauko maganar Al- Maziriy tun daga farko har karshe ya yi, inda ya ce:
قال الإمام: مذهبنا أن هذا الحديث لا يلزم العمل به، واحتج أصحابنا بقول عائشة - رضى الله عنها...".
إكمال المعلم بفوائد مسلم (6/ 431)


Abin lura:
(1) Hadisin A'isha (ra) Mutlaqi ne a sake, Hadisin Ummu Salamah kuma Nassi ne a kayyade. Don haka Nassi kayyadadde ne abin rinjayarwa.
(2) An hakaito MUSTAHABBANCI kin aski da yanke farce daga Imamuna Malik.
(3) Ra'ayin Dr. Ahmad Gumi a wannar mas'ala ra'ayi ne na Hanafiyya masu bin ra'ayi da kin bin Hadisi.


5- Abul Biqa'a Al- Dimyadiy ya ce:
ويستحب لمن أرادها ترك قص شعره وأظفاره إذا أهل ذو الحجة حتى يضحي
الشامل في فقه الإمام مالك (1/ 264)

"MUSTAHABBI ne ga wanda ya yi niyyar Layyah ya bari kar ya aske gashinsa, kar ya yanke farcensa idan jinjirin watan Zul Hijjah ya kama har sai ya yanka layyarsa".

6- Allama Khalil ya nakalto maganar Al- Bajiy wacce ta gabata a farko a cikin littafinsa:
التوضيح في شرح مختصر ابن الحاجب (3/ 278 - 279)

A cikin "Mukhtasar" kuma Khalil din cewa ya yi:
وندب... وترك حلق وقلم: لمضح: عشر ذي الحجة
مختصر خليل (ص: 80 - 81)

"MUSTAHABBI ne barin aski da yanke farce ga mai layyah a kwanaki goma na Zul Hijjah".

HAKA DUKKAN MASU SHARHIN "MUKHTASAR KHALIL" SUN TABBATAR DA HAKA:

7- Abu Abdullah Al- Mawwaq ya ce:
الباجي: عن مالك والمازري عن رواية الأبهري وابن القصار: يستحب لمن أراد أن يضحي إذا رأى هلال ذي الحجة أن لا يقص شيئا من شعره ولا يقلم أظفاره حتى يضحي قالا: ولا يحرم ذلك عليه
التاج والإكليل لمختصر خليل (4/ 372)

"Al- Bajiy da Maziriy sun hakaito daga Malik ta riwayar Al- Abhariy da Ibnul Qassar cewa; MUSTAHABBI ne ga wanda zai yi layyah kar ya yanke komai na gashinsa da farcensa idan watan Zul Hijjah ya kama har sai ya yanka layyah, Al- Abhariy da Ibnul Qassar suka ce: amma ba haramun ba ne".

8- Shaikh Al- Haddab ya ce:
ودليلنا على الاستحباب حديث أم سلمة - رضي الله عنها - أن النبي - صلى الله عليه وسلم - قال «من رأى هلال ذي الحجة، فأراد أن يضحي فلا يأخذ من شعره، ولا من أظفاره حتى يضحي» رواه مسلم والترمذي وأبو داود، وهو حديث حسن صحيح، وهذا نهي والنهي إذا لم يقتض التحريم حمل على الكراهة قاله في التوضيح.
مواهب الجليل في شرح مختصر خليل (3/ 244)

"Dalilinmu a kan MUSTAHABBANCIN (barin aski da yanke farce) shi ne Hadisin Ummu Salamah (ra) ta ce: "Annabi (saw) ya ce: "Duk wanda ya ga jinjirin watan Zul Hijjah, kuma ya yi niyyar layyah to kar ya yi aski, kar ya yanke farce har sai ya yanka layyah". Muslim, Tirmiziy da Abu Dawuda ne suka ruwaito shi, kuma Hadisi ne kyakkyawa ingantacce. Wannan hani ne, hani kuwa idan bai hukunta haramci ba to ana daukansa ne a kan karhanci, haka Khalil ya fada a cikin littafinsa {Al- Taudhih}:
التوضيح في شرح مختصر ابن الحاجب (3/ 278 - 279)

9- Al- Kharashiy ya ce:
(ص) وترك حلق وقلم لمضح عشر ذي الحجة (ش) يعني أنه إذا دخل عشر ذي الحجة فإنه يندب لمن أراد الأضحية أن لا يقلم أظفاره ولا يحلق شيئا من شعره ولا يقص من سائر جسده شيئا تشبيها بالمحرم ويستمر على ذلك حتى يضحي
شرح مختصر خليل للخرشي (3/ 39)

"…Ma'ana; idan goman Zul Hijja sun shiga to MUSTAHABBI ne ga wanda yake son yin layyah kar ya yanke farcensa, kar ya aske wani abu na gashinsa, kar ya yanke komai a jikinsa, don kokkoyon mai Haramar aikin Hajji, zai zauna a haka har sai ya yanka layyarsa".

10- Haka shi ma Shaikh Ulaish ya tabbaar da MUSTAHABBANCIN a cikin sharhinsa mai suna:
منح الجليل شرح مختصر خليل (2/ 474)

• Wannan shi ne abin da ke cikin Littatafan Fiqhun Mazhabar Malikiyya cewa; MUSTAHABBI NE MAI NIYYAN LAYYAH KAR YA YI ASKI, KAR YA YANKE FARCENSA HAR SAI YA YANKA LAYYARSA A RANAR EIDI.
• Saboda haka, abin da Dr. Ahmad Gumi yake korewa akwai shi cikin Mazhabar Malikiyya, kuma shih ya fi rinjaye a kan ra'ayin da shi yake yadawa, wanda ya dace da na masu bin ra'ayi 'Yan Hanafiyya.

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve