*FITOWA TA 4
*DAGA LITTAFIN:-SUFANCI DA AKIDUN SUFAYE.
*JERIN LITTAFAN SUFANCI NA 1
*WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO (hafizahullah)
YADAWA:-www.jibwiskatsina.blogspot.com
Zunnuni Almisri,wani babban Sufi wanda ya rayu a masar,ya
ce,"Sufi shi ne wanda nema baya wahal da shi,kuma rashi baya firgita
shi". Watau shi bai damu da duniya ba balle nemanta ya wahalar da
shi,ko kuma ganin rashi ya firgita shi.
Har ila yau,Abu Turab Annahshabi,wanda shi ma Sufi ne baba,an ji
yana cewa, "Sufi babu abinda yake gurbata shi,kuma kome yana yin
garai-garai da shi." Watau shi ba abinda yake gurbata zuciyarsa,domin
kome ya zo masa na alheri ko sharri ga Allah yake mayar da shi.Shi
kuwa Sahlu binu Abdul Malik Attusturi,kasaitaccen Sufin nan mai
shuhura,cewa ya yi,"Sufi shi ne wanda ya yi garai-garai,ya cika da
tunani,ya koma ga Allah baki dayansa,kuma zinari da hoge suka yi dai
dai a wurinsa.
Har wa yau dai,akwai Alshibli wanda yake cewa,"Sufi shi ne Wanda
ya juyawa mutane baya(ba ya bukatar abinda ke gare su)kuma ya sada
kansa da ubangiji (ta hanyar yawan ibada)."Akwai kuma Abu Sa'id
Aljazzar Wanda ya ce,"Sufi shi ne wanda Allah ya tsarkake zuciyarsa ta
cika da haske,kuma ya tsunduma cikin mayen zikirin Ubangiji."
Wannan kadan me nan daga maganganun Sufaye dangane da ma'anar
Sufi. A hakika,ra'ayin Sufaye ya sha bamban dangane da ma'anar Sufi da
Sufanci har ta kai ana iya cewa ko wane Sufi yana da nasa Sufancin na
kansa.Bari mu saurari abinda suke fadi game da ma'anar Sufanci.
Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 5 insha Allah.
Abu Aisha journalist
Jibwis Social Media Katsina
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve