Sunday, 14 May 2017

ZATIN TAWAYE WA HALATTACCIYAR HUKUMA BA KAFIRCI BA NE A IDANUN SHARI'AR MUSULUNCI:


'Yan bidi'ah da dama ne suka dauki yi wa halattacciyar hukuma tawaye a matsayin kafirci! Wannan shi ne ma ya sa suke kafirta Sayyidina Mu'awiya tare da wadanda suke tare da shi Allah Ya kara musu yarda; saboda kawai rundunar shi Mu'awiya ta yaki rundunar halartacciyar hukumar Sayyidina Aliyyu Bin Abi Talib Allah Ya kara masa yarda a yakin da aka sani da sunan "Yakin Siffin" (Siffin wani bangare ne a yanzu na birnin Raqqah a cikin kasar Siriya kusa da kan iyakar kasar Iraq) wanda a cikin wannan yakin ne aka kashe Sahabi Ammar Bin Yasir Allah Ya kara masa yarda Sahabin da ke cikin rundunar Sayyidina Aliyyu Bin Abi Talib.
Allah Madaukakin Sarki Ya bayyanar da matsayin bangaren 'yan tawaye da kuma bangaren halattacciyar hukuma a cikin suratul Hujurat aya ta 9-10 a inda Ya ce: ((وان طائفتان من المؤمنين اقتتلوا فأصلحوا بينهما فان بغت احداهما على الاخرى فقاتلوا التي تبغي حتى تفيء الى امر الله فان فاءت فأصلحوا بينهما بالعدل وأقسطوا ان الله يحب المقسطين. إنما المؤمنون اخوة فأصلحوا بين أخويكم واتقوا الله لعلكم ترحمون)). Ma'ana: ((Idan bangarori biyu daga Muminai suka yaki juna ku yi sulhu tsakaninsu, idan dayansu ya yi zalunci a kan dayan to ku yake wanda ke zaluncin har sai ya koma ga umurnin Allah, in ya koma sai ku sulhunta tsakaninsu a bisa adalci, ku yi adalci lalle Allah Yana son masu adalci. Ai Muminai 'yan'uwan juna ne sai ku yi sulhu tsakanin 'yan'uwanku, ku ji tsoron Allah akwai tsammanin za a muku rahama)). Kun gani a nan duk da kasancewar wadannan bangarori biyu sun yaki junansu bangare daya ya yi wa daya tawaye ya zalunce shi to amma Allah Ya kira su da cewa su Muminai ne 'yan'uwan juna, kuma Ya yi umurni da a yi sulhu a tsakaninsu.
Da wadannan bayanai da suka gabata ne za mu fahimci cewa 'yan bidi'ar da ke kafa hujja da Hadithi na 447 da Imamun Bukhariy ya ruwaito, na 2916 da Imamu Muslim ya ruwaito cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce: ((ويح عمار تقتله الفئة الباغية يدعوهم الى الجنة ويدعونه الى النار)). Ma'an: ((Ayya Ammar! Bangaren jama'a masu tawaye za su kashe shi, yana kiran su zuwa Aljannah, suna kiran shi zuwa Wuta)). Wadannan yan bidi'ar da ke kafa hujja da wannan Hadithi domin su kafirtar da Sayyidina Mu'awiyah da sauran wadanda suka yi yaki cikin rundunarsa sun bace cikin wannan fahimta tasu sun bar hanyar Shari'ar Musulunci; saboda sam babu lazimi tsakanin wadannan abubwa guda biyu: yi wa halattacciyar gwamnati tawaye da kafirce wa Allah Madaukakin Sarki musamman ma idan aka san cewa ko wanne daga cikinsu mujtahidi ne cikin matsayar da ya dauka shi kuwa Mujtahidin da yake da cancantar Ijtihadi koda kure ya yi cikin hakikanin al'amarin to yana da lada guda na ijtihadinsa kuma Shari'ah ba za ta kama shi da laifin kurensa ba; saboda Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce: ((اذا حكم الحاكم فاجتهد فأصاب فله أجران وإذا حكم فاجتهد فأخطا فله اجر واحد)). Ma'ana: ((Idan mai hukunci ya yi hukunci ya yi ijtihadi sannan ya dace da daidai to yana da lada biyu, idan kuma ya yi hukunci ya yi ijtihadi ya yi kure to yana da lada daya)). Saboda haka duk da yake a nan su suna kiran Ammar ne zuwa ga abin da zai iya kaiwa ga shiga Wuta; watau suna kiran shi ne zuwa ga yi wa halattaccen Khalifan Musulmin Duniya tawaye to amma dai wannan kiran nasu sun yi shi ne gini a kan halattaccen ijtihadinsu ke nan ba su da zunubi cikinsa.
Allah Ya taimake mu Ya kare mana imaninmu Ya yi mana baiwar fahimtar shari’arSa. Ameen.

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve