Sunday, 14 May 2017

ANYI KIRA GA YAYAN GIDAN QADIRIYYA AKAN SU YI HAKURI SU SULHUNTA DA JUNA


Wannan kira ya fito daga bakin Babban Limamin
Masallacin tunawa da Sheikh Jafar Mahmud
Adam dake Tudun Murtala kuma Shugaban
Kungiyar Izala na Jihar Kano Sheikh, Dr. Abdullahi
Saleh Pakistan.
Shehin Malamin yayi wannan kira ne a lokacin da
yake gabatar da Hudubar Jumu'a ta jiya a
masallacin nasa dake Tudun Murtala inda ya roki
yayan wannan gida akan su dubi girman Allah su
yi hakuri kuma su kai zuciya nesa domin su dinke
6arakar dake tsakanin su wadda takai wannan na
jifar wancan da miyagun kalamai a tsakanin su.
Malam ya cigaba da cewa ba dai-dai bane ga
yayan wannan gida suke yin abubuwa
makamantan wannan, kasancewar gidan nasu
gida ne mai dogon tarihi akan abinda ya shafi
Ilimin addinin Musulunci kuma har yanzu idan
za'ayi maganar Malaman da suka hidimta wa
Addinin Musulunci a Kasar nan bal ma a Nahiyar
Africa dole ne a saka asalin mai wannan gida
Babban Malami Sheikh Nasiru Kabara (r.h)
Wanda kowa a cikin Ku yana son yayi yana son
yayi koyi da shi kuma shi ba' a san shi da irin
wannan tashin-tashina ba.
Kazalika Malamin ya bayyana cewa rikici a gidan
kowa akwai shi saboda haka matukar yan siyasa
wadanda basu taso gidan Ilimi da tarbiya ba zasu
samu sa6ani a tsakanin su kuma su dinke shi a
tsakanin su ba tare da kowa yaji kan su ba to
babu shakka ku da kuka taso gidan Ilimi da
tarbiya Ku yafi cancanta akan Ku da Ku sulhunta
kan ku ba tare da kowa ya sani ba domin kune
kuke da tarin Ayoyi da Hadisai da suka yi nuni da
haka.
Malam ya kara da cewa ko kadan ba ma jin
dadin irin wadannan al'amura dake faruwa domin
wani salo ne da zai sa makiyan mu makiya
addinin Musulunci su koma gefe suna yi mana
dariya suna cewa a junan mu ma muna yakar kan
mu da kan mu duk da cewa suma akwai rikici da
fitintinu a tsakanin su amma su nasu rufe yake a
tsakanin su.
Daga karshe Malam yace duk da irin sa6anin
fahimtar dake tsakanin mu da ku ba zai hana
idan mun ga wani abu da zai cutar da ku mu yi
muku nasiha kuma mu ankarar da ku ko ba
komai zamu sauke nauyin da Allah Ya dora mana
na sulhunta tsakanin Muminai, ya kara da cewa
da cewa da mun san wata hanya da zamu bi mu
isar muku da wannan sakon kuma ku yi aiki dashi
ba wannan ba yace Wallahi da shi zamu bi.
Muna rokon Allah Ya yi mana maganin rikice-
rikicen dake tsakanin Musulman duniya Ya kuma
hada kawunan mu akan gaskiya.
Lawal Mamman Bilbis
Jibwis Social Media Kano
12/05/2017.

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve