Bambanci mafi girma da ke tsakanin Ahlus Sunnah da 'Yan Bidi'ah shi ne: Su Ahlus Sunnah suna yarda, suna kuma yin imani da dukkan wani labari da Annabi mai tsira da amincin Allah ya bayar; ko dai ta hanyar nassin Alkur'ani mai girma, ko kuwa ta hanyar nassin ingantattun hadithansa masu daraja. To amma su 'Yan bidi'ah suna yarda ne kawai da abin da ya dace da abin da zuciyarsu ke so, abin da kuwa ya saba wa son zuciyarsu to shi wannan ba za su taba yarda da shi ba, ba za su taba yin Imani da shi ba koda kuwa nassin Alkur'ani mai girma ne ya zo da shi, koda kuwa nassin ingantaccen hadithin Annabi ne ya zo da shi. Ga wasu misalai nan:-
1. Imamut Tirmiziy ya ruwaito hadithi na 3747, da Imamu Nasaa'iy hadithi na 8194, da Imamu Ahmad hadithi na 1675, da Imam Ibnu Hibban hadithi na 7002, da Imam Bazzar hadithi na 1020, da Imam Abu Ya'alaa hadithi na 835, da Imam Ibnu Abi Shaibah hadithi na 32,609 da isnadi sahihi daga Abdurrahman Bin Auf Allah Ya kara masa yarda ya ce:-
((ابو بكر في الجنة، وعمر في الجنة، وعثمان في الجنة، وعلي في الجنة، وطلحة في الجنة، والزبير في الجنة، وعبد الرحمن بن عوف في الجنة، وسعد بن ابي وقاص في الجنة، وسعيد بن زيد بن عمرو بن نفيل في الجنة، وابو عبيدة بن الجراح في الجنة)).
Ma'ana: ((Abubakar yana cikin Aljannah, da Umar yana cikin Aljannah, da Uthman yana cikin Aljannah, da Aliyyu yana cikin Aljannah, da Talhah yana cikin Aljannah, da Az-Zubweir yana cikin Aljannah, da Abdurrahman Bin Auf yana cikin Aljannah, da Sa'ad Bin Abi Waqqas yana cikin Aljannah, da Sa'id Bin Zaid Bin Amr Bin Nufail yana cikin Aljannah, da Abu Ubaidah abin Jarrah yana cikin Aljannah)).
Ahlus Sunnah sun amince sun kuma yi imani da cewa wadannan Sahabbai goma dukkansu 'yan Aljannah ne da nassin Annabi mai tsira da amincin Allah a kan hakan, to amma akwai 'yan bidi'ar da suka karyata wannan labari na Annabi mai tsira da amincin Allah suka bi son zuciyarsu, suka ce babu mutumin kirki mumini cikin wadannan Sahabbai goma in banda Aliyyu Bin Abi Talib kadai ba!
2. Annabi mai tsira da amincin Allah ya ba wa Duniya labarin cewa: Matansa uwaye ne ga Muminai, kamar yadda nassin wannan labari ya zo cikin Suratul Ahzab ayah ta 6 kamar haka:-
((النبي اولى بالمومنين من انفسهم وازواجه امهاتهم)).
Ma'ana: ((Annabi ne ya fi Muminai cancantar kawunansu, kuma matansa uwayensu ne)).
Ahlus Sunnah sun yarda da wannan ayah, sun yi imani da gaskiyar da labarinta ke kunshe da shi, suna kuma son dukkan matan Annabi suna kuma daukansu uwaye a gare su, to amma an sami wasu daga cikin 'yan bidi'ah da ba su yarda da cewa Nana A'isha, da Nana Hafsah uwaye suke gare su ba, su a gurinsu matan banza suke wadanda suka bar addinin Mudulunci suka kafirta!
3. Annabi mai tsira da amincin Allah ya bayyana wa Duniya cikin Alkur'ani mai girma cewa mahaifin Annabi Ibrahim alaihis Salam makiyin Allah ne. Su kuma Ahlus Sunnah sun yarda, sun kuma yi imani da cewa lalle mahaifin Annabi Ibrahim din makiyi ne na Allah kuma dan Wuta. To amma kusan dukkan 'yan bidi'ah sun bi son zuciyarsu a nan suka ce wannan da Allah Ya kira shi da cewa shi ne mahaifin Annabi Ibrahim cikin Alkur'ani ba shi din ba ne mahaifin nasa, a'a mahaifin shi wani daban ne ba wannan ba; saboda da haka mahaifin Annabi Ibrahim alaihis Salam ba kafiri ba ne makiyin Allah duk kuwa da cewa Allah ya ce cikin suratut Taubah ayah ta 114:-
((وما كان استغفارابراهيم لابيه الا عن موعدة وعدها اياه فلما بين له انه عدو لله تبرا منه)).
Ma'ana: ((Neman gafarar da Ibrahim ya yi mahaifinsa bata kasance ba illa wani alkawari ne kawai da ya alkawarta masa, to amma lokacin da ta bayyana gare shi cewa shi makiyin Allah ne sai ya barranta daga gare shi)).
4. Annabi mai tsira da amincin Allah ya bayyana wa Duniya a cikin Alkur'ini mai girma cewa: Kanin mahaifinsa mai sunan yanka: Abdul Uzzaa mai sunan kunya Abu Lahb dan Wuta ne shi. Kuma su Ahlus Sunnah sun amince da hakan, sun kuma yi imani da hakan, ba tare da sun ce don me Allah ba zai cusa wa bappan Annabi mai tsira da amincin Allah imani ba cikin zuciyarsa, don me Allah zai sanya shi Abu Lahab duk kuwa da cewa kanin uba yake ga Annabi mai tsira da amincin Allah a cikin Wuta?
5. Annabi mai tsira da amincin Allah ya bayyana wa Duniya cikin Alkur'ani cewa: Matar Annabi Nuhu alaihis Salam, da Matar Annabi Lutu alaihis Salam dukkansu su biyun 'yan Wuta ne su. Kuma su Ahlus Sunhah sun amince da hakan, sun kuma yi imani da hakan, ba su kuma ce: don me Allah bai cusa imani cikin zukatan wadannan mata na Annabawan Allah ba? Don me Allah zai sanya su cikin Wuta ba zai sanya su cikin Aljannah tare da mazansu ba?
6. Annabi mai tsira da amincin Allah ya bayyana wa Duniya cikin Alkur'ani mai girma cewa: Daya daga cikin 'ya'yan Annabi Nuhu alaihis Salam kafiri ne da yaki yin imani da mahaifinsa. Kuma su Ahlus Sunnah sun amince da hakan, sun kuma yi imani da hakan, ba su kuma ce: don mene ne Allah ba zai cusa imani cikin zuciyarsa ba domin ya kasance tare da mahaifinsa cikin kubuta daga halakar Tuufan, ya kuma kasance tare da mahaifin nasa cikin gidan Aljannah ba?
Lalle shi Musulmin kirki har kullum zai tsaya a inda Shari'ah ta ce ya tsaya, sawaa'un hakan ya dace da abin da zuciyarsa ta fi so ko kuwa bai dace da abin da zuciyarsa ta fi so ba. Allah muke roko da Ya taimake mu Ya tabbatar da mu cikin shiriyarSa. Ameen.

No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve