![]() |
Alhaji Maigari Usman Malala |
Daga: Musa H. Musa
A jiya Lahadi Majalisar agaji ta Jihar Gombe ta gabatar da taro a Gadam Karamar Hukumar Kwami wadda yahada dukkanin masu rike da mukamai a matakin jiha da kuma wakilan Division da National.
Dayake jawabi Directan Agaji ta jihar Gombe Alhaji Maigari Usman Malala Ya hakaito taron kasa da akagabatar a funtua tare da zayyano dukkanin Rahoton da National ta bayar kan dokokin aikin agaji,
Tare da Umartan Ofishin Secretary da Organizing Secretary da Intallegent su gabatar da jawabai akan ayyukan da suka shafesu ,
Sannan Ya gabatar da jawabai kan watan ramadan da ayyukan da akasaba gabatarwa a watan tare da Kira ga Al'umma da subaiwa yan agaji hadin Kai Yayin gabatar da aikin,
Sannan aka karbi shawarwari akan ayyukan da Akasa agaba domin cin nasarar aikin,
Muna Addu'ar Allah ya basu nasara cikin ayyukan da suke gabatarwa, Ameeen.
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve