![]() |
Sheikh Abdullahi Bala Lau |
Daga: Ibrahim Baba Suleiman
An tafi hutu har zuwa bayan sallah insha Allah
Kungiyar IZALA ta kammala Ziyara mai taken 'Zuwa da kai yafi sako' zango na hudu a jihar Plateau wadda itace jiha ta 16 cikin jerin jihohin Naijeriya 37 harda Abuja, da tawagar ta kudiri niyyar ziyarta a tarayyar Naijeriya da yardan Allah.
Ziyarar wadda Shugaban Izala Sheikh Abdullahi Bala Lau ke jagoranta, tare da wakilcin shugabanni, Malamai' Yan agaji da kuma ma'aikatan kungiyar, ta ziyarci jihohin Kaduna, Niger, Abuja da Plateau a wannan wannan satin cikin zango na hudu.
Manufar ziyayar dei shine, duba ayyukan Da'awa, Kadarorin kungiya tare da zama da dukkan 'ya'yan kungiyar domin tambaya ko bada shawara kai tsaye ga shugaban kungiyar ta kasa, ka na daga bisani a ziyarci shugabannin Bangaren mulki a duk jihar da aka ziyarta domin kyautata alaka.
A halin yanzu tawagar ta dakatar da ziyarar har zuwa bayan sallah, domin fiskantar harkokin tafsiri da malamai zasu gabatar a watan Ramalana insha Allah.
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve