Daga: Ibrahim Baba Suleiman
Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya Alh. Muhammad Sa'ad Abubakar III, ya bada Sanarwan ganin jinjirin watan Ramadan a kasar Naijeriya.
Sarkin yace anga Jinjirin watan a garuruwa da dama Daga cikin Sassan Kasar, wanda ya kawo karshen watan Sha'aban, kuma gobe Asabar Musulman Najeriya zasu tashi da azumin watan Ramadan insha Allah.
Da fatan Allah ya mana jagora, ya karbi dukkan ibadun da za'a gabatar a wannan wata mai tarin Albarka. Amin.
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve