1. Wajibi ne kowa ya so Annabi mai tsira da amincin Allah, ya kuma so koyi da shi, ya kuma yarda da dukkan abin da ya inganta daga gare shi ba tare da jin kuncin hakan ba a cikin zuciyarsa.
2. Wajibi ne kowa ya yi koyi da Annabi mai tsira da amincin Allah a cikin aqidarsa, da ibadarsa, da mu'amalarsa iya karfinsa; watau a bisa Ka'idar fadar Allah Madaukakin Sarki: فاتقوا الله ما استطعتم Ma'ana: ((Ku ji tsoron Allah iya karfinku)).
3. Daga cikin madogararmu a kan abin da muka fada akwai fadar Allah a cikin suratul Ahzab aya ta 21 لقد كان لكم في رسول الله أسوة حسنة لمن كان يرجو الله واليوم الاخر Ma'ana ((Hakika akwai koyi mai kyau game da manzon Allah a gare ku; watau ga wanda ke tsammanin Allah da ranar Karshe)). Da kuma fadarsa a cikin suratun Nisa'i aya ta 65 فلا وربك لا يؤمنون حتى يحكموك فيما شجر بينهم ثم لا يجدون في أنفسهم حرجا مما قضيت ويسلموا تسليما Ma'ana ((A'a ina rantsuwa da Ubangijinka cewa ba za su yi imani ba har sai sun maida kai mai yin hukunci cikin sabanin da suka yi sannan kuma ba za su ji wani kunci ba a cikin rayukansu game da abin da ka hukunta su kuma mika wuya mikawa)). Da kuma Hadithi na 44 da Imam Muslim ya ruwaito daga Anas Dan Malik cewa manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce: لا يُؤْمِن احدكم حتى اكؤن أحب اليه من ولده ووالده والنَّاس اجمعين Ma'ana ((Dayanku ba zai yi imani ba har sai na kasance na fi soyuwa a gare shi a kan dan shi da mahaifin shi da kuma dukkan Mutane)). Da kuma wasu nassoshi da yawa masu kama da wadannan.
4. Kuma saboda irin wadannan nassoshin ne ma ne Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya ce cikin Majmuu'ul Fataawaa 24/202 وأما من تبينت له السنة فظن ان غيرها خير منها فهو ضال مبتدع بل كافر Ma'ana ((Amma duk wanda Sunna ta bayyana a gare shi sannan ya yi tsammanin cewa waninta ya fi ta alheri to lalle shi batacce ne kuma dan bidi'a, kai kafuri ma)).
Allah muke roko da Ya tabbatar da dugaduganmu a kan daidai har kullum.

Ameen.
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve