Sunday, 30 April 2017

WAJIBI NE MUSULMI YA TSAYA INDA SHARI'A TA CE YA TSAYA:

Dr Ibrahim Jalo Jalingo

Ba daidai ba ne musulmi ya wuce-gona-da-iri game zatin Annabi mai tsira da amincin Allah; saboda nuna kauna da girmamawa a gare shi; Imamul Bukhaarii ya ruwaito hadithi na 3,445, da Imamu Muslim hadithi na 1,691 cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce:-
((لا تطروني كما أطرت النصارى ابن مريم انما انا عبد فقولوا: عبد الله ورسوله)).
Ma'ana: ((kada ku wuce gona da iri cikin yabona, kamar yadda Kirista suka wuce gona da iri cikin yabon Dan Maryam, ni ba kowa ba ne face bawa, ku ce: bawan Allah kuma manzonSa)).
Ga dai abin da Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce wa al'ummarsa na hana su wuce iyakar Sahari'ah cikin yabonsa; watau su yi wata karya game da shi da nufin yabo da girmamawa. Sai dai kuma abin bakin ciki a nan shi ne kadan ne kwarai daga cikin wannan Al'ummah tamu suke yin amfani da wannan gargadi na Annabi mai tsira da amincin Allah.
Misali: Ya zo cikin littafin Jawaahirul Ma'anii 1/147 nassi kamar haka:-
((اول ما خلق الله تعالى روح محمد صلى الله عليه وسلم ثم نسل الله منها أرواح الكائنات ثم كون الله من جسد النبي صلى الله عليه وسلم أجساد الملائكة والأنبياء والأقطاب)).
Ma'ana: ((Farkon abin da Allah Ya halitta shi ne ran Muhammad mai tsira da amincin Allah, sannan ya halitta sauran rayukan halittu daga shi (wannan ran) sannan kuma Allah Ya halicci jikkunan Mala'iku da Annabawa da Manyan waliyyai daga jikin Annabi Mai tsira da amincin Allah))!
Tabbas babu gaskiya cikin wannan magana da ta zo cikin wannan littafi na Jawaahirul Ma'aniy; domin ijama'in Musulmin kwarai ya kullu a kan cewa Annabi mai tsira da amincin Allah yana daga cikin zurriyyar Annabi Adam ne ba wai shi Annabi Adam din ba ne yake daga cikin zurriyyarsa; saboda Allah Madaukakin Sarki Ya ce cikin Suratul Hijri aya ta 28-29 :-
((وإذ قال ربك للملائكة اني خالق بشرا من صلصال من حما مسنون. فإذا سويته ونفخت فيه من روحي فقعوا له ساجدين)).
Ma'ana: ((A lokacin da Ubangijinka Ya ce wa Mala'iku lalle ne ni Mai halittan wani dan adam ne daga wani irin laka busashshe, daga wani irin bakin tabo jirkitacce, to idan na daidaita shi, kuma na busa raiNa cikin shi, to sai ku fadi kuna masu yi masa sujjada)).
Sannan kuma Ya ce cikin suratus Sajdah aya ta 7-8 :-
((الذي أحسن كل شيء خلقه وبدا خلق الانسان من طين. ثم جعل نسله من سلالة من ماء مهين)).
Ma'ana: ((Shi ne wannan da Ya kyautata dukkan kome da Ya halitta shi, sannan Ya fara halittar jinsin mutum ne da laka, daga nan Ya yi zurriyyarsa daga wani irin daskararren jini da kuma wani irin ruwa kaskantacce)).
Allah Ya taimake mu Ya tsare mana imaninmu.
 Ameen.

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve