*******
Shi Shekarau dama ba Ahalus Sunna Bane (Idan nace Ba Ahalus-Sunna ba Ina Nufin ba Yana tare da 'yan Izala bane). D'an boko ne wanda yafi karkata zuwa ga 'yan Ummah.
Amma yana nuna tamkar yana tare da Ahlus Sunnah don haka Kifawar farko lokacin da ta watse tsakanin Ahlus Sunnah da Kwankwaso (ya zamanto basa shiri), sai Ahlus Sunnah suka rika Wa'azozi suna goyon bayan Shekarau.
Ahlus Sunna Suna Wa'azozi suna Ahir kar a sake a zabi Kwankwaso, a dai-dai lokacin ne Su Abdul Jabbaru suka hura tambarin Wa'azi suna Tsoratarwa akan Shekarau suna kar a zabi Shi d'an Izala ne.
A kano (a wancen Lokaci), Idan aka ce maka ga d'an Izala to kamar mu a zariya ace maka ga d'an Shi'a.
Saboda haka suka rik'a Cewa, Shekarau d'an Izala ne, (Muna da dimbin kasusuwan da Abdul Jabbaru yayi ta tsoratarwa akan kar a zabi Shekarau d'an Izala ne).
Su Malam Ja'afar kuma Sukayi ta wa'azi suna goyon bayan Shi (Shekarau), har yaci zabe.
Ana nan da tafiya tayi tafiya, Gwamnati ta kafu, Sai Shekarau ya fara fitar da hali, a takaice dai ya dawo kai tsaye. Ya had'a kai da 'yan darika, 'yan Tijjaniyansu da 'yan Kadiriyarsu ya zama duk abinda zai zama kyautatawa ce da mutuntawa ce ga Ahlus Sunnah Shekarau baya Goyon Bayanshi.
Duk abinda zai marawa 'yan Darika ya zama Shekarau shi yake goyon baya, ana nan Sai 'yan Shi'a suka fake da Masarautar kano Suka fake da 'yan Darik'a sai ya zama A fakaice Gwamnatin Kano (Karkashin Jagorancin Shekarau) tana tare da 'yan Shi'ah da 'yan Dariku da Masarautar kano, suka b'ata da Ahlus Sunna wayanda su suka hankid'ata suka zuba mata fetur ta tashi.
Aka dawo aka ci amanar Ahlus Sunnah, aka dawo ana yakarsu, to a lokacin ne Gwarzon Namu Malam Ja'afar Mahmud Adam ya fito yace, Sam bai yarda ba Shine aka fito aka fara mishi gori.
Aka Ce, ai Yaci Albashi, na Gwamnatin Kano kuma baiyi aiki ba, ai an biya mishi Kujerar aikin hajji da Umara, ai an anje kama Gidajen Alhazzai Shekara kaza da ta wuce, da shi aka kama, ai yana ji yana gani dashi akayi zalunci aka raba, ai bayyi magana ba Sai bana da yaji za'a yi zaluncin ba da shi ba. Haka akayi ta maganganu a jaridu da makamantansu.
To wad'an nan dalilai Sai suka biyo baya dukkan mu Ahlus Sunnah a Nigeriya, Sai muka sha alwashin duk wani mai mulki dake zalunci baza'a goyi bayanshi ba.
Idan Jama'ah basu manta ba Gwamna Ahmad Muhammad Makarfi har gidana yazo wai yazo kamfen zaiyi tazarce.
Nace, Uhm Ni din? Ashe makarfi yasan dani a duniya? me ya kawo shi yazo ya b'ata min Suna ne? Gari ya waye in wayi gari ina kashe sababbin Kuddi ace ai jiya Gwamna yaje gidansa.
Nace, to ace mishi Nima na kafa Gwamnatin talauci a gidana, kalmar da na fadawa d'an aikenshi kenan.
To adai-dai wannan lokacin Suma su Malam Ja'afar suna da nasu gwarzon suna da kuma wanda basu yarda a zab'a ba.
To me ya faru? Yaje yayi wa'azi a Bauchi ya dawo, (Shi k'adai ya dawo a mota), tun daga Bauchi har Kano. Ranar Alhamis.
Akazo akayi wa'azi Wannan Wa'azin anyi shine don a bayyana Matsayin Malaman Ahlus Sunnah game da Siyasa da kuma zaben da za'a fuskanta a Ranar Asabar da murya d'aya akayi magana.
Da aka gama Shi (Sheikh Ja'afar), Yayi Wa'azi Sama Sama ne, Yace, to shi nashi Sak'on Sai Gobe Jumu'ah Idan anzo Hudubar Jumu'ah anan zai fad'i nashi sak'on.
To Masu mulkin Jahar (Su Shekarau), Suna da yakini d'ari bisa d'ari (100%), Cewa, Zai ce k'ar a zabe su, kuma in yace kar a zabe su sun tabbatar da Cewa, Sai dai su sace akwati ba dai su ci ba don haka aka wayi gari Jumu'a an harbeshi. An kashe shi.
Kafin ya hau mimbari da zai yi Hudubar lalata musu wannan k'uri'ar don haka muke da Tuhuma Mai k'arfi akan Shekarau.
Marigayi Shiekh Awwal Adam Albani Ya gabatarda Wannan Muhadara a Garin Zariya A Ranar Assabar 11/09/ 2009 Muhadara Mai taken Waya kashe Shiekh Jafar kasit na Ukku.
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve