Daga Abbas Musa Kganuwa
Ba kasafai ake samu a cikin al’umma dace da shugaba mai hangen nesa da kuma ganin an ciyar da al’umma ba, musamman al’ummar Musulmai da suke yin da’awar Sunna a Afirka ba. Hasalima a wannan lokacin da shuwagabanni suke cikin ru?ani na rikice-rikicen matsayi da kuma ganin mai za su samu mai kuma za su ri?e da kuma ganin sun handame da kuma yin babakere a cikin al’amuran al’umma, sai ga shi ita ?ungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Allah Ya amsa mata bu?atarta da addu’o’in da ta da?e ta ro?on Allah na Ya azurta ta da shuwagabanni masu tsoron Allah, tausayi da kuma hangen nesa cikinsu har da Sheikh Bala Lau.
A cikin wannan rubutu da zan yi ba zai iya wadatar da abubuwan amfani da ci gaba da wannan bawan Allah yake gabatarwa ba, da kuma irin ?imbin nasarori da ya samu a cikin ?an ?an?anin lokaci ba.
Kafin in fara magana a kan nasarori da kuma irin ci gaban da ya kawo sai na fara kawo mana abubuwa da dama da muka rasa da kuma dalilai da ya sanya muka ?auki wannan jarumin shugaba muka ce zamuyi tsokaci na musamman a kansa ba.
?aya daga cikin matsalolin musulmin Najeriya ita ce, ina muka dosa, bayan kasancewar mun san cewar ga daga inda muka fito. Rashin sanin takamaimai wurin da muka dosa shi ne babban matsalar wannan al’umma. Hakan ta faru ne tun daga lokacin da muka rasa manyan jagororin al’umma kamar su Sheikh Abubakar Mahmud Gumi (Allah Ya yi mishi rahama), Alhaji Ahmadu Sardaunan Sokoto (Allah Ya yi mishi rahama). Rashin wa?annan bayin Allah ya kawo ta?ar?arewar jagoranci da kuma sanin ina musulmai suka nufa.
Matsaloli ba su da adadi wanda wannan al’umma take fama da su, kama daga ha?in kai na al’ummar musulmai da kuma ?o?arin neman ganin an cike gurabun da ya kamata a ce musulman wannan ?asar sun cike na wuraren ilimi da mu?amai da ma kowane irin fanni.
Musulmai a wannan ?asar ba su da wata babbar makarantar jami’a ta zamani da za ta ware wani bangaren na al’umma kodai maza zalla ko kuma mata zalla da zasu karantar da ‘ya’yansu ilimi na ha?i?a da kuma tarbiya ta addinin musulunci.
Wannan al’umma ta rasa yadda za ta kawo wata hanya da zata iya dogaro da kanta na ganin ta kafu da ?afarta wurin ganin an samu abubuwan more rayuwa da kuma abubuwan da al’umma zata ri?a dogaro da shi wurin tafiyar da al’amuranta na yau da kullum.
Idan muka dawo ta ?angaren Ahlussunnah a wannan yanki namu na Arewa sai muga cewar mune koma baya matu?a a cikin harkokin tafiyar da hanyar yin da’awa da kuma yadda ya dace ace muke tafiyar da al’amuranmu na yau da kullum.
Mas’alolin suna da yawa amma bari in taba mana wani bangare da yake damun duk wani Musulmi da yake cikin Arewa, shi ne maganar Asibitin Musulmai wanda ya amsa sunansa, kuma wanda lallai idan kana da kowace irin matsala idan ka je wannan wuri bu?atarka ta biya. Musamman idan muka ce za muyi maganar cakuduwar maza da mata da kuma samun kwararrun likitoci da kuma kayan aiki na zamani sai muga cewar lallai bamu da irin wannan asibiti.
Ya ake ?aukar aiki, wa kuma ya dace a ?auka wannan itama matsala ce mai zaman kanta da take damun musulmai kasancewar a baya saboda su Malam Abubakar Mahmud Gumi ana ?o?arin ganin an bai wa musulmai ha??insu, amma bayan rasuwarsa sai aka rasa wanda ya damu da ganin an baiwa musulmai guraben da ya dace da su.
Su wane suke wakiltarmu a fannoni da mu?amai a wannan ?asar, su wane ne suke yin magana da yawun musulmai da kuma ganin an magance ita irin wannan matsalar. Musulmai da suke Majalisar Wakilai da na Dattijai nawa muke da su, sannan suna yin abubuwan su domin kare muradun al’umma ne ko kuma suna yi domin ganin sun wakilci kawunansu da iyalan su da kuma iyayen gidajensu ne?
Mu hadu a kashi na biyu
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve