*Rahotanni sun ce mahukunta a Saudiyya sun zane wani Yariman gidan sarautar kasar bayan da aka same shi da aikata laifi.
*Wannan na zuwa ne makwanni kadan bayan da aka kashe wani jinin sarautar kasar bisa laifin kisan kai. Amma kawo yanzu ba a bayyana suna ko ainahin laifin da yariman ya aikata ba.
*Sai dai ba kasafai ake samun jinin gidan sarautar da laifi ba ko kuma a yanke musu irin wannan hukunci.
*Wasu masu amfani da shafukan sada zumunta a kasar sun yi farin ciki da hukuncin, suna masu cewa ya nuna yadda shari'ar Musulunci ke bi ta kan kowa. Kawo yanzu ba a bayyana wannan labari a hukumance ba.
*Tsohon ministan tsaro, Musliu Obanikoro ya dawo da Naira Miliyan 100 cikin kudaden da ake tuhumarsa akan ya ci.
Duk da cewa miliyan 600 hukumar EFCC ta ke bukata daga hannun sa Obanikoro yace bashi da wadannan kudade yanzu, Miliyan 100 ne kawai za'a iya samu daga hannun sa.
Obanikoro ya karbi Biliyan biyu ne da ga hannun Dasuki cikin kudin siyan Makamai.
*Majalisar zartarwar Najeriya ta amince da kirkiro karin jami'o'I 8 da kungiyoyi daban-daban da majami'u ke mallaka.
*Amincewar dai ta biyon bayan zaman majalisar zartawane kan lamarin bisa shawarin hukumar kula da jami'o'i ta Najeriya NUC.
*Ban da daya daga jami'o'in 8 mai suna "CROWN-HILL" da ke jihar Kwara,duk sauran 7 din a kudancin Najeriya su ke.
*Kazalika an ba su lasisin gwajin aiki don nuna gamsuwa na tsawon shekara 3 da kuma mika ragamar rainon su ga jami'o'I mafi kusa da su.
*'Yan sanda a babban birnin Najeriya Abuja, sun jefa hayaki mai sa kwalla kan reshen dalibai na kungiyar 'yan Shi'a a Abuja da su ka yi wata muzahara don neman sako shugaban su Ibrahim Elzakzaky.
*'Yan sandan dai na zargin 'yan kungiyar 'yan Shi'a da gudanar da zanga-zanga ba tare da neman izini ba da hakan kuma ya na barazana ga tsaro a cibiyar Najeriya.
*Kwana Guda bayan taron masu ruwa da tsaki daga Naija Delta da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayi a Abuja, tsagerun yankin sun fasa wani bututun mai mallakar kamfanin NNPC.
*Sojojin dake aikin samar da tsaro a Yankin sun sanar da jin karar fashewa a tashar Batan dake Jihar Delta lokacin da aka kai harin da misalign karfe 12.
*Jami'in yada labaran Kamfanin man Najeriya Garbadeen Muhammed ya tabbatar da kai harin.
*A jihar Sokoto da ke Najeriya, manyan sarakuna daga ciki da wajen kasar ne ke halartar bukukuwan cika shekaru goma da nadin Alhaji Sa'ad Abubakar a matsayin sarkin musulmi. Mai martaba sarkin Kano Muhammad Sanusi na biyu ne shugaban gudanar da bukukuwan.
Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
03/Safar/1438
03/November/2016
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve