Friday, 4 November 2016

LABARAIA TAKAICE


*Hukumar tara haraji ta Nijeriya FIRS ta ce ta samu fiye da masu neman aiki dubu 700 da ke neman guraben aikin da aka tallata na mutum 500 a hukumar.

*Shugaban Hukumar Tunde Fowler ne ya bayyana hakan ga kwamitin majalisar wakilan kasar kan sauraron koke-koken jama'a.

*Tunde Fowler, ya kara da cewa, sama da mutum 2, 000 daga cikin masu neman aikin na da digiri daraja ta daya, kuma dukkansu sun cancanci a dauke su.

*Gwamnatin Najeriya ba za ta janye ko fice daga kotun duniya ba da ke birnin Haque.

*Ma'aikatar wajen Najeriya ta baiyana haka da nuna kotun ta duniya na da muhimmanci wajen kare muradun miliyoyin al'ummar duniya.

*Ma'aikatar ta lura da yadda wassu kasashen Afurka da su ka hada da Burudi, Afurka ta kudu da Gambia su ka bayyana aniyar su ta ficewa daga kungiyar.

*Babban Mai Taimaka Wa Shugaban Kasa a Hulda da Majalisar Tarayya, Hon. Suleiman Abdurrahman Kawu Sumaila, ya bayyana cewa a yanzu haka ya na Iya bakin kokarin sa wajen tuntubar Shugabannin Majalisar Tarayya da kuma kwamitocin da ke da ruwa tsaki dangane da batun amincewa da lamuni na kudi da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai karbo, har na Dala milyan 29.9.

*Tsohon shugaban Hukumar kwastam Abdullahi Dikko Inde ya dawo da sama da Naira Biliyan 1 asusun gwamnatin Najeriya.

*Kudin ya na daga cikin Kudaden da Inde ya waske dasu a lokacin yana shugaban hukumar Kwastam na kasa.

*Duk da haka hukumar EFCC ta na jiran sauran kudade daga hannun Dikko Inde.

*Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, wanda shine shugaban kwamitin taron bikin cikar Sarkin Musulmi shekaru goma a karagar mulki, ya mika godiyarsa ga Allah na kasancewar Mai Alfarma Sa'ad Abubakar a matsayin Sarkin Musulmi.

*Mai Martaba Sanusi, wanda ya bayyana hakan a wurin bikin cikar Sarkin Musulmin shekaru goma akan mulki, ya kuma kara da cewa za su ci gaba da yin biyayya ga Sarkin Musulmin kasancewar sun yaba da salon mulkinsa don haka a koda yaushe ya umarce su da yin ayyuka za su bi umarninsa.

Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
04/Safar/1438
04/November/2016

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve