Wednesday, 2 November 2016

LABARAI A TAKAICE


*Majalisar dattawan Najeriya ta dakatar da muhawarar bukatar karbo bashi da shugaba Buhari ya mika zauren majalisar da ya kai dala biliyan 30.

*Majalisar dai za ta bukaci karin bayani kan muhimmancin karbo lamunin daga ketare.

*Biyo bayan muhawarar da ta nuna rashin goyon bayan sayar da kamfanin iskar gas na Najeriya don samun kudin aiwatar da kasafin kudi da raya tattalin arziki, ya nuna gwamnatin Najeriya ta dauki zabin ciwo bashi daga ketare don samun kudin da za ta biya a hankali.

*Ministan kudi Kemi Adeosun ta ce Najeriya ba ta da zabi fiye da amso lamuni don gwamnati ba za ta jira sai gangar fetur ta murmure kafin ta samu kudin aiwatar da ayyukan raya kasa ba.

*Babban hafsan rundunar sojan kasan Najeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya nuna muhimmancin aiki tare da rundunar 'yan sanda don gamawa da burbudin 'yan ta'addan Boko Haram.

*Buratai da ke magana a ziyarar da ya kai wa babban sufeton 'yan sanda Ibrahim Kpotum Idris, ya ce ya na da kyau rundunonin biyu su ke atisaye da musayar dabaru don cimma wannan aiki na wanzar da zaman lafiya.

*Darajar Naira ta karu da samun kimanin Naira 4 na daraja a canjin tsakanin bankuna da ya sanya dala daya ta dawo naira 304 daga wajajen Naira 308.

*Hakanan a kasuwar canji ma Nairar ta samu tagomashi na ragin Naira biyu inda a ke sayar da dala kan naira 465 maimakon Naira 468 da a ka sayar a farkon mako.

*Kwanakin baya dai Naira ta samu matukar koma baya kan dala inda ta doshi kusan Naira 480 kan dala daya.

*Matukar hakan ya ci gaba da dorewa da sakin dalar daga babban banki,Nairar za ta ci gaba da dagowa kamar yadda masana tattalin arziki su ka bayyana.

*Rahotanni sun nuna cewa hukumar kula da rundunar 'yan sanda ta kasa ( PSC) da kuma majalisar tarayya sun cimma matsaya kan sabanin da suka samu kan shirin daukar 'yan sanda 10.000 aiki, lamarin da ya janyo aka dakatar da shirin.

*Da yake tabbatar da haka, Shugaban Kwamitin 'Yan sanda na majalisar Dattawa, Sanata Abu Ibrahim ya ce sun warware sabanin da ke tsakani majalisa da hukumar PSC inda suka amince a yi amfani da kananan hukumomin wajen raba guraben aikin.

*Rundunar 'yan sandan jihar Borno ta tabbatar da mutuwar wasu mutane tara sakamakon tashin bam din da ya auku a jiya Talata.

Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
02/Safar/1438
02/November/2016

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve