*Rahoton hukumar kare hakkin bani adama ta Human rights watch ya nuna cin zarafin mata ta lalata da su ta hanyar fin karfi a sansanonin 'yan gudun hijira a Najeriya musamman a arewa maso gabas.
*Wannan ya kara nuna halin takaici da 'yan gudun hijirar ke ciki baya ga batun rashin wadatar abinci.
*Tuni dai shugaba Buhari ya ba da umurnin bincika rahoton don daukar matakin da ya dace.
*Jaridar DailyTrust ta binciko rahoton da ke nuna annobar zazzabin cizon sauro ta barke a sassan Najeriya ka ma daga Sokoto, Kaduna zuwa Gombe.
*Rahoton ya nuna daya bisa ukun masu rasa ran su daga cutar a manya da kuma daya bisa hudu na jarirai a kasashe masu zazzabin duk a Najeriya a ke samun akasin.
*A Sokoto ma rahoton ya nuna yadda mutane ke amfani da ganyen gwanda da sauran su wajen maganin da hakan ya sanya wassu matasa shiga sana'ar sayar da ganyen.
*A Kaduna kullum mutane na garzayawa asibiti da kokawa kan fama da zazzabin. Hakanan fiye da mutum 100 kan shiga babban asibitin gwamnatin tarayya a Gombe don duba su kan zazzabin cizon sauro a kullum.
*Dr.Nasiru Sani Gwarzo na ma'aikatar lafiya ta tarayya ya ce gwamnati ta dauki matakan ci gaba da raba gidajen sauro da fadakar da jama'a muhimmancin kawar da ruwa da kan kwanta don hana karuwar sauro.
*Dr. Ahmed Gana na hukumar lafiya matakin farko ta Gombe ya ce mutane ba sa amfani da gidan sauro da a ke raba mu su kyauta amma dai gwamnatin jihar za ta kara odar magunguna don amfanin al'umma.
*Ba Zai Yiwu Ba A Ce Kasar Da Aka Dauki Tsawon Shekaru Ana Lalata Kuma A Yi Tsammanin Za A Gyara Ta Cikin Kankanin Lokaci, Don Haka Al'ummar Nijeriya Su Kara Hakuri Da Gwamnatin Buhari, Sakon Sarkin Daura Ga Al'ummar Nijeriya
*Gwamnatin jihar Kebbi tare da hadin gwiwar wata cibiya dake kasar Amurka mai suna 'Moses Lake Medical' tare da kungiyar Likitocin Nijeriya reshen jihar Kebbi, sun fara aikin duba marasa lafiya da kuma yi musu aikin tiyata kyauta.
*Liktocin za su kwashe makonni biyu suna yi, inda aka kiyasta kowane yini za su duba marasa lafiya kimanin dari biyar tsakanin asibitin Gwamnati dake Birnin Kebbi da kuma Babban Asibitin gwamnati dake garin Zuru.
Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
01/Safar/1438
01/November/2016
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve