*Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce bai umurci wani daga mukarraban sa, ya ba da Cin hanci ga alkalai don murde shari'ar zabe ba.
*Buhari na mayar da martani ne kan zargin da biyu daga alkalan da a ke tuhuma da zarmiya su ka yi cewa ministan sufuri Rotimi Amaechi ya tunkare su da ba da hanci don murde shari'ar zabe da ke gaban su.
Shari'un dai sun hada da na Rivers,Abia da Akwa Ibom.
Buhari ya nesanta kan sa daga ba da irin wannan umurni da nuna shi zai zama mutum na karshe da zai ambaci wani abu mai kama da haka.
*Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya ce gwamnatin Najeriya ba ta da sha'awar damke tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan.
*Osinbanjo da ke magana a wani taro a birnin Texas na Amurka,ya ce gwamnatin ba ta da sha'awar kama mutum ko ta halin kaka, bisa ma'ana sai bayan tabbatattun hujjoji.
*Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje yace bazai nemi takarar ahugaban kasa ba a shekarar 2019. Ganduje ya bayyana hakan ranar Asabar a jihar Sokoto a yayin wani taro na masu ruwa da tsaki a jam'iyyar APC, ya kuma kara da cewa ba zai nemi takarar shugabancin kasan ba duk da cewa wasu na yi masa tayin hakan.
*Gwamnan ya kara da cewa zai kiyaye yin hakan domin gudun aikata kuskure kamar yadda wadanda suka gabace shi suka yi.
*Rahotanni daga garin Maiduguri sun nuna cewa dakarun sojojin Nijeriya sun bindige wani dan kunar bakin wake dake dauke da bama-bamai har guda biyu a jikin sa, a lokacin da ya yi yunkurin shiga sansanin 'yan gudun hijira na Bakassi dake garin Maiduguri a safiyar jiya.
*Ikirarin da kungiyar tawayen Houthi ta 'yan Shi'an Yaman ta yi cewa ba Makkah ta yi niyyar kai wa hari ba,amma kan filin saukar jiragen sama na Jeddah ne kuma ta samu nasara, ya jawo fushi daga kasashen duniya.
*Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna damuwa ga wannan mummunan harin.
*Hukumomin Saudiyya dai sun ce sun kakkabo makamin mai linzami kilomita 65 a wajen garin Makkah.
*Hukumomin sun ce in ma kan filin saukar jiragen sama na Sarki Abdul-aziz ne,to ya nuna rashin sanin ya kamata don cibiya ce ta zirga-zirgar alhazai daga dukkan fadin duniya.
*Majalisar SarkinMusulmi ta bada sanarwan yau litinin ne za'a fara duba sabon jinjirin wata na safar. Duk wanda ya gani sai ya sanar da shugabannin sa har zuwa gare su.
HOTO: *Gwamnan Jihar Niger Alh Abubakar sani Bello yake baiwa Sabon Sarkin Borgu Alh Mohammed sani Haliru Dantoro sanda a matsayin Sarkin yanka, kuma Sarki na 17 a masarautar.
Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
29/Muharram/1438
31/October/2016
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve