*Ministan Harkokin Cikin Gida, Abdurahman Danbazau ya tabbatar da cewa gwamnatin Naijeriya ta baiwa tsohon mai bawa Shugaban kasa shawara kan tsaro, Sambo Dasuki damar halartar Jana'izar mahaifinsa, Marigayi Ibrahim Dasuki amma ya ki amincewa da yin haka.
*Danbazau ya nuna cewa tun lokacin da marigayin ke jinya an nemi Sambo Dasuki ya ziyarce shi amma ya nuna cewa zai ci gaba da yi masa addu'a daga inda ake tsare shi.
*A na ci gaba da tsare Sambo Dasuki a hannun jami'an tsaron farin kaya DSS inda shari'ar sa ke ci gaba da gudana.
*Shugaban Rundunar 'Yan sanda ta Kasa, Ibrahim Idris ya bayyana dalilin da ya sa 'yan sanda suka bude wuta kan mabiya Shi'a a Kano inda ya nuna cewa 'yan Shi'an na dauke da makamai a lokacin arangamar.
*Ya ci gaba da cewa rundunar ba za ta kyale wasu tsiraru da ke neman kawo rudani a cikin kasa ba su kashe jami'an tsaro da sunan neman 'yancinsu inda ya kara da cewa nauyin rundunar ce na kare dukiyoyi da rayukan 'yan Nijeriya.
*Kungiyoyin kwadagon Najeriya sun gudanar da zanga-zanga a gaban majalisar dokokin Najeriya don nuna rashin amincewa ga yunkurin sayo motocin hawa ga 'yan majalisar da a ka yi lissafin darajar su ta kai Naira 3.6.
'Yan majalisar wakilan 360 na son samun motoci ne kirar FIJO.
*Hukumar bunkasa hanyoyin samun kudaden shiga da raba arzikin kasa ta Najeriya ta nuna gamsuwa ga muradin gwamnatin Najeriya na neman karbo lamunin Dala biliyan 29 daga ketare.
Shugaban hukumar Shettima Abba Gana ya ce hakan ne kawai mafita ga shawo kan karancin kudin ketare a Najeriya.
*Wani babban hafsan sojan Nijeriya ya rasa ransa sakamakon harin da 'yan Boko Haram suka kai musu
*Mamacin mai suna B.U. Umar, wanda ke rike da mukamin Liyutanal Kanal, shine kwamandan Bataliya ta 114 na rundunar sojojin Nijeriya. Sannan kuma ya rasa ransa ne a safiyar litinin tsakanin garin Bita da Piridang a lokacin da suke hanyarsu ta zuwa garin Yola babban birnin jihar Adamawa.
Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
16/Safar/1438
16/November/2016
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve