Wednesday, 16 November 2016

ANYI KIRA GA YAN AGAJI SU CI GABA DA NUNA HALLAYYA NA GARI.

Rundunar Agajin Izala reshen jahar Borno ta yi kira ga 'Ya'yanta da su ci gaba da nuna hallayya na gari a duk inda suka kasance.

Kiran ta fito ne daga bakin jami'in yada labarai na rundunar agajin Mal. Tukur Umar Buratai a hirar da yayi da manema labarai.

Rundunar Agajin ta nemi 'Yayan ta da su ci gaba da nuna hallayya na gari a duk inda suka kasance, kamar dai aka horar da shi da dabi'u kyawawa da rundunar Agajin take yi a koda yaushe.

Rundunar Agajin ta bayyana cewa tana taka muhimmiyar rawa wurin magance ayyukan ta'addanci, Ta hanyyar baiwa 'Ya'yan ta kyakkyawan tarbiya, tace kyakkyawan tarbiya da girmama na gaba ne ke hana yara shiga aikin ta'addanci.

Rundunar tace, babban aikin 'Dan agaji shine bada taimakon farko ga mara lafiya shiray filin wa'azi da bada tsaro a wurin, rikon amana, kyawawan halayya da girmama na gaba.

Saboda haka muna kira ga Membobin mu da su ci gaba da nuna kyakkyawan hallaya da girma ma na gaba dasu, kamar yanda aka san su.

Muna addu'ar Allah ya sanya mana a mizani, ya bamu zaman lafiya mai daurewa, Amin.

Jibwis Borno Branch, 14/11/2016

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve