Sunday, 13 November 2016

LABARAI A TAKAICE


*Hukumar alhazan Najeriya NAHCON ta fara duba aiyukan ofisoshin alhazan jihohi da mu su lasisin aiki da hakan zai kara inganta kula da jin dadin alhazai.
Sanarwa daga jami'in labarun hukumar Uba Mana ta ce tuni hukumar ta ratsa arewa maso yammacin kasar da jihar Bauchi inda ta duba kayan aiki da ofisoshin alhazan .

*Hukumar dai za ta ba da lasisi mai matakai 3 A B C da hakan zai nuna fifiko wajen rabiyar kujerun alhazai a aikin hajji mai zuwa na 2017.

*Gwamnatin Najeriya Ta Musanta Batun Cewa Saida Ta Baiwa 'Yan Boko Garam Dala Milyan 21 Kafin Suka Sako 'Yan Matan Chibok Guda 21

*Mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu, wanda ya bayyana hakan, ya kara da cewa labarin ba shi da tushe kawai farfaganda ce na wasu kafafun yada labarai.

*Daruruwan 'yan ta'addan Boko Haram sun yi saranda ga rundunar hadin guiwar yaki da Boko Haram din ta yankin tafkin Chadi.

*Kakakin rundunar da ke da helkwata a Ndjamena ta Chadi,Kanar Mohammed Dole ya baiyana hakan da nuna cin karfin 'yan ta'addan ya tilasta su ajiye makamai.

*Hadin guiwar kasashen ya taimaka ainun wajen rage karfin yakin Boko Haram da a da kan kwace garuruwa da sace mutane.

*Sabon gwamnan jihar Edo a kudu maso kudancin Najeriya  Godwin Obaseki ya sha rantsuwar shiga ofis da amsar ragama daga tsohon gwamna Adams Oshiomhole.

*Ba a samu canjin jam'iyya ba a zaben don APC mai mulki ta ci gaba da mulki kan jam'iyyar adawar jihar PDP da dan takarar ta Pastor Ize Iyamu.

*Yanzu dai ido ya koma kan zaben jihar Ondo don gadon mulki daga gwamna Olusegun Mimiko na PDP. Za a yi zaben 26 ga watan nan.

*Gidan Talabijin mallakar tsohon shugaban kasa Atiku Abubakar TV GOTEL ta sallami kashi 50 bisa 100 na Ma'aikatanta.

*Hakan dai yana da nasaba ne da tabarbarewan tattalin arzikin kasa da kasa Najeriya ke fama da shi kamar yadda masana suka ce.

*Bayan haka wata kamfanin sa mai suna Adama foods da ke sarrafa ruwan ruba da lemun zaki ta bi sahun wancan na talabijin din inda ta rage Ma'aikata.

*Sabon Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump Ya Goge Furucin Da Ya Yi A Shafinsa Na Yanar Gizo Na Cewa Zai Hana Musulmai Shiga Kasar Amurka Muddin Ya Ci Zabe

Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
13/Safar/1438
13/November/2016

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve