*Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya sake ganawa da shugaban majalisar dattawan Najeriya Bukola Saraki a fadar ASO ROCK Abuja.
*Ganawar wacce itace ta biyu a mako daya;ta mayar da hankali ne kan batun amincewa da amso lamunin Dala biliyan 29 daga ketare da majalisar ba ta amince da bukatar ba.
*Yanzu dai da alamu sashen zartarwar Najeriya zai sake dawo da bukatar don samun amincewar majalisar.
*Kungiyar kiyaye hakkin dan adam ta "Amnesty International " ta na yunkurin neman a yafewa wani dalibi dan Najeriya Chigioke Obioha da kasar Singapore ta damke da laifin safarar miyagun kwayoyi.
Singapore dai kan yanke hukuncin kisa kan wadanda a ka samu da irin wannan laifi.
A baya dai irin wannan sanya baki ko yunkuri bai ceci 'yan Najeriya da a kama daga hukuncin kisa ba.
*'Yan kunar bakin wake sun yi yunkurin kai hari kan Maiduguri a arewa maso gabashin Najeriya.
*Matan 3 sun gamu da daukar mataki daga 'yan sanda daidai kauyen Ummarari kan hanyar Damboa inda su ka harbe su.
*Wannan shine sabon salon da 'yan Boko Haram su ka bullo da shi wajen tada hankalin al'ummar Maiduguri da a yanzu su ka dawo haiyacin su daga kashe - kashe ko miyagun hare-hare na 'yan ta'addan.
*Amurkawa da dama na ci gaba da zanga-zanga don nuna bacin rai da nasarar da Donald Trump ya samu na lashe zaben shugabancin kasar.
*Trump dai ya bayyana zanga-zangar da rashin adalci kazalika kuma da tunzura jama'a su nuna ma sa kiyayya da kafafen labaru ke yi.
*Zababben Shugaban na Amurka Donald Trump ya gana da shugabannin Jam'iyyarsa ta Republican domin dinke barakar da ke tsakaninsu bayan yawancin shugabannin Jam'iyyar sun juya ma shi baya a lokacin yakin neman zaben shi.
Trump dai zai karbi mulki a hukumance a watan Janairu na badi.
*Mai shafin sada zumunta na Facebook Mark Zuckerberg ya kare shafin saboda zargin da aka yi masa cewa Facebook ne ya rika watsa labaran kanzon-kurege da suka bai wa Donald Trump nasarar zama shugaban Amurka.
Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
12/Safar/1438
12/November/2016
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve