Sunday, 13 November 2016

ASALIN AKIDAR KUNGIYAR IZALAH.


Har kullum karkatattu suna ganin ba za su iya tallan hajarsu ta bata da son zuciya ba har sai sun yi wa wadanda suke ganin cewa su abokan husuma ne a gare su: kage da yarfe da sharri tukun, har sai sun dora musu abin da ba su fada ba tukun!!

Shekarun baya Sufaye sun yi ta mana irin wannan yarfen suna gaya wa Duniya cewa wai mun ce babu waliyyai, mun ce kada a yi wa Iyaye biyayya, da dai sauran nau'ukan yarfe da kage.

**********

Abin da masu da'awah ke cewa shi ne: ko ma mazhabar wa kake bi to wajibi ne a kanka ka san cewa haramun ne a kanka ka san cewa ga hadithi nan na manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya inganta cikin wata mas'ala daga cikin mas'aloli sannan ka bar yin aiki da wannan hadithin ka koma ka yi riko da ijtihadin wani malami cikin malamai komin girmansa da yawan ilminsa, lalle haramun ne ka yi haka matukar dai ijtihadin wannan malamin ya saba wa wannan nassi na Annabi, wannan kuwa shi ne maganar ko wane mutumin kirki cikin malaman Musulunci; sawaa'un Imam Malik ne, ko Imam Abu Hanifah, ko Imamush Shafi'iy, ko Imam Ahmad, ko Imam Auzaa'iy, ko Imam Laith, ko Shaikhul Islam Ibnu Tamiyyah, ko Sheikh Uthmsn Bin Fodiyo, ko Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, ko ma wane ne shi matukar dai yana tsoron Allah yana kuma girmama manzon Allah mai tsira da amincin Allah da maganarsa.

********

Da ba don harkar batarwa irin ta Shaidan ba, ai a fili yake cewa mu membobin kungiyar Izala tun daga tashin da'awarmu a farkon fari wannan hanyar gaskiya ita ce hanyarmu; wannan shi ne ma ya sa muka haramta dukkan wani nau'i na laya, duk kuwa da cewa abin da ke rubuce cikin mazhabar Malikiyya shi ne: rataye laya abu ne da ke halal matukar dai abin da ke cikin layar ayoyin Alkur'ani ne ko kuwa wasu maganganu ne da aka san ingancin ma'anarsu!
Haka nan a lokacin da babban Shaihinmu Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya yarda da littafin da Sheikh Ahmad Sanusi Gumbi ya rubuta ya kuma kore dawowar Annabi Isa a cikinsa, mu mun nuna rashin yardarmu da wannan hanya da shaihinmu ya dauka, mun ma rubuta masa raddi a kan wannan mazhaba da ya bi. Tabbas wannan shi ne asalin da'awar kungiyar Izala mai yawan albarka; watau gabatar da abin da ya inganta daga manzon Allah mai tsira da amincin Allah a kan dukkan wata mazhaba ta wani mutum, ko a kan dukkan wata fatawa ta wani mutum.

**********

To amma sai ga shi a yanzu wasu sun lalace sun bar wannan Mabda'i da wannan Aqidah da Manufa ta kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah sun koma suna ta bin hanyar 'yan bidi'ah ta nuna ta'assubanci ga ra'ayin wani mutum, ko ra'ayin gungun wasu mutane a lokacin da ta tabbata cewa ingantaccen hadithin manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya saba masa.

*******

Allah muke roko da Ya tausaya wa al'ummarmu Ya cusa musu son fifita maganar Annabi mai tsira da amincin Allah a kan ijtihadin ko wane mujtahidi matukar dai ijtihadin ya saba wa maganar shi manzon Allah mai tsira da amincin Allah. Ameen.

Dr Ibrahim Jalo Jalingo

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve