Monday, 7 November 2016

Izala ta jajantawa rundunar Sojoji bisa rasuwar Kanal Abu Ali


Shugaban Izalar Naijeriya Sheik Abdullahi Bala Lau, ya mika jajen ta'aziyyar kungiyar Izala ga rundunar sojin Naijeriya bisa rasuwar Gwarzon Soji Kanal Muhammad Abu Ali.
Shugaban ya kara mika ta'aziyyar kungiyar ga Ilahirin Al'ummar Jihar Kogi, tare da 'Iyalai da -yan uwa da abokan arziki, da mahaifin marigayin tsohon gwamnan jihar Bauchi Burgediya Janar Abu Ali mai ritaya wanda shine sarkin masarautar Bassa "ETSU BASSA" a jihar Kogi.
Kanal abu Ali wanda A yau Litinin ake jana'izar sa tare da da wasu sojoji hudu, sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suke kokarin dakile wani harin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai kan barikin sojin kasar na 119 da ke garin Malam Fatori a Jihar Borno.
Shugaba Sheikh Abdullah Bala Lau yace rasa gwarazan Soji irin Su kanal Abu Ali ba karamin rashi ne a kasa ba, Sheikh yace saboda da jajircewar sa akan aiki yasa A shekara ta 2015 Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai, ya yi wa Muhammad Abu-Ali karin girma daga Manjo zuwa Laftanar Kanar tun kafin ya kai shekarun samun karin girman, saboda jaruntar da ya nuna da ta kai ga kwato yankuna da dama daga hannun mayakan na Boko Haram.
Sheikh Bala Lau yace yana addu'ar Allah ya jikan dukkan musulmai muminai wadanda suka rasa rayukan su a fagen daga, Allah kuma ya kare sauran sojojin mu da suke filin daga ya basu nasara a dukkan lamuran su. Amin.
Jibwis Nigeria
07/Safar/1438
07/November/2016

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve