*Shugaban Rundunar Sojan Kasa, Janar Tukur Burutai ya tabbatar da cewa Mayakan Boko Haram na kaddamar da sabbin hare hare ne saboda suna samun tallafi a asirce daga wasu Tsirarun 'yan Nijeriya.
*Ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da ya karbi bakuncin wata tawagar sojojin Amurka inda ya nemi hadin kan kasashen duniya da al'ummar Nijeriya wajen ganin an murkushe sauran mayakan Boko Haram din.
*Haka nan kuma, Janar Burutai ya kasa boye tausayinsa a yayin jana'izar Kanal Ali wanda. Boko Haram suka kashe inda ya rika kuka.
*Alkalin Alakalai mai barin gado, Mai Shari'a, Mahmud Mohammed ya nuna cewa hukumar da ke kula da kotuna ta kasa ( NJC) ta yanke shawarar dakatar da Alkalan nan guda bakwai da ake zargi da rashawa ne don tabbatar da 'yancin bangaren shari'a.
*Ya ci gaba da cewa daga yanzu hukumar NJC ta yanke shawarar dakatar da duk wani ma'aikacin kotu da ke fuskantar tuhuma kan wani laifi kamar yadda tsarin mulkin kasar nan ya tanada.
*Tsohon Gwamnan Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa ya bayyana dalilin rashin halartar bikin cikar Sarkin Musulmi 10 kan sarauta inda ya nuna cewa masarautar ba ta ba shi goron gayyata ba.
*Ya ce, a matsayinsa na Garkuwan Sokoto kuma wanda shi kadai ya tsaya wa Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Saad II aka ba shi sarautar amma kuma masarautar ba ta mutunta ta shi ba.
*Bafarawa ya yi zargin cewa wadanda suka shirya bikin ne suka kulla wannan makarkashiya na kin bashi wani rawa da zai taka a yayin bikin yana mai cewa ya kauracewa taron ne don gudun aukuwar wani abin Jin kunya.
*Kwamitin majalisar dattawan Najeriya mai kula da sansanonin gudun hijira zai bincika labarin karancin ruwa da kayan kiwon lafiya a sansanonin 'yan gudun hijira a Borno da jihar Adamawa.
*Shugaban kwamitin Sanata Abdulaziz Nyako shi ya baiyana wannan aniya da nuna damuwa kan duk da makudan kudin da a ke warewa amma sansanonin sun zama cikin karncin ruwan sha da magunguna.
*Kwamitin dai tuni ya ziyarci wassu daga sansanonin.
*Gwamnatin jihar Plateau da ke arewa ta tsakiyar Najeriya na shirin fara karbar haraji daga masu sayar da magungunan gargajiya a jihar.
*Sauran sassan da za su biya harajin sun hada da na noma,sufuri,kiwon lafiya da kuma duk mutanen da su ka kai biyan haraji a jihar.
*Hukumar tara haraji ta jihar ta ce wannan hanya za ta magance karbar haraji fiye da sau daya daga hannun mutane amma wanda ya kaucewa biyan harajin zai fuskanci mataki mai gauni.
*A talatar nan za a gudanar da babban zaben Amurka don gadon mulki daga bakar fata na farko da ya mulki kasar Barack Obama tun shugaban kasar na farko George Washington.
*Amurkawa dai za su darje su zabi wa imma mace ta farko da za ta zama shugaban kasar Hillary Clinton ta jam'iyyar Democrats ko dan kasuwa mai dari-dari da baki Donald Trump na Republican.
*Dama an fara gudanar da zaben tsakanin mutane da wa imma za su shagaltu da wassu lamura ranar zaben ko za su yi tafiya.
Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI ta wanke Hillary Clinton daga laifin aikata wasikun gwamnatin Amurka ta amfani da akwatin sakonni na kashin kai.
Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
08/Safar/1438
08/November/2016
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve