Monday, 7 November 2016

LABARAI A TAKAICE


*Wata fitacciyar jarida da ake bugawa a Birnin London, mai suna Africa Voice, ta karrama Hon. Abdulmumin Jibrin da kambin Gwarzon Dan Majalisa na Afrika, na 2016.

*Jaridar dai ta ba shi wannan lambar yabo ne dangane da irin gwagwarmayar da ya ke yi wajen magance cin hanci da rashawa da almundahana a Najeriya.

*Wani matashi a birnin Kano da ke arewacin Najeriya mai suna Mukhtar Adam Fasaha ya kirkiri wata mota mai amfani da makamashin hasken rana.

*A na fargabar mutum 10 sun rasa ran su a sakamakon kifewar kwale-kwale a Kacha da kuma gobarar tankar mai a Mokwa a jihar Neja.

*Hatsarin kwale-kwalen dai  ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 7 inda na gobarar tankar mai ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 3.

*Wadanda su ka rasa ran su a hatsarin kwale-kwale mata ne da ke hanyar tafiya gona inda ita kuma tankar man da ke dauke da gas ta aukawa wassu motoci ne inda ta kama da wuta.

*A yau Litinin ne hukumomin sojin Najeriya ke jana'izar kwamandan rundunar sojin kasar ta 272 mai kula da tankokin yaki, Laftanar Kanar Muhammad Abu Ali, tare da wasu sojoji hudu.

*Kwamandan da sauran sojojin hudu sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suke kokarin dakile wani harin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai kan barikin sojin kasar na 119 da ke garin Malam Fatori a Jihar Borno.

*Haka ma wasu sojojin hudu sun samu raunukka yayin da mayakan Boko Haram 14 suka halaka a cikin artabun na yammacin ranar Asabar.

*A shekara ta 2015 ne Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai, ya yi wa Muhammad Abu-Ali karin girma daga Manjo zuwa Laftanar Kanar tun kafin ya kai shekarun samun karin girman, saboda jaruntar da ya nuna da ta kai ga kwato yankuna da dama daga hannun mayakan na Boko Haram.

*Jama'a na ci gaba da tura ta'aziyyar rasuwar barden sojojin Najeriya na yaki da Boko Haram Laftanar Kanar Abu Ali .

*Muhammad Abu Ali wanda dan jihar Kogi ne kuma dan tsohon gwamnan mulkin soja na jihar Bauchi Burgediya Janar Abu Ali,ya sadaukar da ran sa wajen yaki da 'yan ta'addan Boko Haram da hakan ya sanya cin nasarar kwato garuruwa da dama da tura 'yan ta'addan can cikin dajin Sambisa.

*Gwamnan Kogi Yahaya Bello ya mika ta'aziyya ga mahaifin marigayin Burgediya Janar Abu Ali mai ritaya wanda shine sarkin masarautar Bassa "ETSU BASSA" a jihar Kogi.

*Laftanal Kanal Muhammad Abu Ali , Hazikin Soja Ne Da Ba Za A Tabaa Mancewa Da Shi Ba, Inji Shugaban Naijeriya Muhammadu Buhari

Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
07/Safar/1438
07/November/2016

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve