Wednesday, 19 October 2016

Sako Daga Shugaban Izala na Africa - Bala lau


"Ina kira ga 'yan uwana musulmai da cewa kowa yaji tsoron Allah, ku Sani cewar Allah Ta’ala yana kallon duk abinda muke fada ko muke rubutawa, walau na gaskiya ko kuma son rai, mu Sani Mala’iku Rakibu da Atidu suna rubutu babu kakkautawa. Watarana sai an tambaye mu dukkan abun da muka aikata a lokacin rayuwar duniya.
Yi kokari ka aikata alheri tare da kyakkyawan aiki wannan shi zai maka amfani ranar gobe kiyama.
Gaba, Kiyayya, Hassada da bakin ciki wannan ba sabon abu bane ga Malaman Sunnah, alama ce ta Allah yana karban ayyukan da ake yi, mu dai fatan mu shine Allah ya karbi ayyukan da muke, tare da Ikhalasi.
Da fatan Allah ya bamu dacewa.

Dan uwanku a musulunci: Abdullahi Bala Lau".
An dai ruwaito wannan kira ne daga Shehin Malamin yayi wannan  a shafin shi na Fezbuk.

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve