*Boma-bomai biyu sun tashi a Maiduguri jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya inda fitinar Boko Haram ta fi yi wa illa.
*Bom na farko ya tashi a gaban sansanin 'yan gudun hijira na Bakassi da ke hanyar Damboa inda akalla mutum 5 su ka rasa ran su.
*Daya bom din ma ya tsahi kan wannan hanyar ce a gaban DAFFON MAI NA NNPC.
*Motocin daukar marassa lafiya na karakaina a yankin da jami'an tsaro su ka killace.
*Garin Maiduguri ya samu salama don karya alkadarin 'yan ta'adda na Boko Haram da a ka yi, inda a yanzu hare-haren su ka koma na kunar bakin wake ko dana bom.
*Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin sa ba za ta binciki tsohuwar gwamnatin Rabi'u Musa Kwankwaso ba duk da yadda wassu gwamnatocin ke binciken ayyukan da su ka gabata.
*Ganduje ya ce da ayyukan da a ka kammala da wadanda ba a kammala ba a jihar, gwamnatin sa za ta inganta su don amfanin al'ummar jihar.
*Tsohon shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar wakilan Najeriya Abdulmumin Jibrin ya bukaci jami'an yaki da cin hanci su gaggauta daukar mataki kan shugabannin majalisar wakilai kan zargin da ya yi mu su na aringizo a kasafin kudi.
*Jibrin a sanarwar da ya fitar ta cika kwana 100 tun wannan zargi da ya yi, ya ce ba zai yi kasa a guiwa ba kan abun da ya ce gwagwarmayar yaki da cin hanci.
*Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya ce wasu gwamnonin yankin Arewa Maso Gabas na shirga karya akan Yan gudun hijira da ke jihohinsu domin Su samu gudunmawa akan hakan.
Gwamnan ya ce kusan dukkan Yan gudun hijiran suna yankunan jihar Borno ne sannan wadanda suke wasu yankunan ma da kasashen ketare duk suna karkashin jihar Borno ne.
*Kungiyar Izala tace zata bibiyi lamarin taqaddamar limanci wanda ya barke a Masallacin Sultan Bello tsakanin magoya bayan Sabon limamin masallacin Dakta Khalid da magoya bayan Dakta Ahmad Gumi wanda har ya jawo 'yan sanda suka harba Barkwanon tsohuwa
*Shugaban JIBWIS na kasa Imam Abdullahi Bala Lau ya shaidawa manema labaru a Kaduna cewa za su wanzar da sulhu tsakanin dukkan sassan saboda a ci gaba da gudanar da ibada cikin natsuwa a masallacin mai dimbin tarihi.
HOTO: Dr. Ahmad Gumi a lokacin da ya kaiwa Sheikh Abdullahi Bala Lau ziyara a gidansa dake kaduna.
Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
28/Muharram/1438
30/October/2016

No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve