Thursday, 19 October 2017

*FITOWA TA 4.
*Daga Littafin:-AKIDAR YAN SHI'A DANGANE DA SAHABBAI.
*JERIN LITTAFAN SHI'A NA 2.
*WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO(hafizahullah).
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com

Akidar yan Shi'a dangane da Sahabbai ba ta tsaya a kan
kafirta su ba kawai,amma suna ganin cewa su Sahabbai su ne mafiya
sharrin halittar Allah,wal iyazu billahi!! Kuma suna kudure cewa imani
da Allah da Manzonsa ba ya tabbata sai an barranta daga gare
su,musamman dai manya-manya daga cikinsu kamar Abubakar da Umar da
Usman da Aisha da Hafsa da sauran ire-irensu.Muhammad Bakir
Almajlisi,daya daga cikin manyan malaman Shi'a, yana cewa: "Akidarmu
ta barranta ita ce cewa mu mun barranta daga gumaka hudu:Abubakar da
Umar da Usman da Mu'awiya;da kuma mataye hudu:Aisha da Hafsa da Hindu
da Ummul Hakam.kuma muna barranta daga dukkan mabiyansuda magoya
bayansu;kuma muna kudure cewa su ne mafiya sharrin halittar Allah a
bayan kasa;kuma cewa imani da Allah da Manzonsa da Imamai ba ya
tabbata sai bayan an barranta daga makiyansu(yana nufin Sahabbai)."
[A duba HAKKUL YAKIN na Almajlisi,519].

Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 5 Insha Allah.

Abu Aisha journalist.
Jibwis Social Media Katsina.

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve