Thursday, 19 October 2017

*FITOWA TA 20
*Daga Littafin:-SUFANCI DA AKIDUN SUFAYE.
*Jerin Littafan Sufanci Na 1.
Wallafar:-Prof.Umar Labdo(hafizahullah)
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com

1-Nakasa a jikin mutum,kamar yarinta.Zuciyar yaro ba za ta iya ganin
hakika ba saboda yarintarsa.

2-Gurbatar zuciya da yawan aikata sabo da muggan ayyuka.

3-Shagaltar zuciya ga barin neman hakika,kamar mutumin da ba ya tunani
game da Allah to har abada zuciyarsa ba za ta ga hakika ba.

4-Yimkewar zuciya da wani kuduri da ya gabata,kamar mutumin da ya taso
tun yarintarsa yana kudure da abinda ya ga iyayensa suna yi,to wannan
abu sai ya hana WA zuciyarsa ganin hakika.

5-Rashin sanin hanyar bi domin kaiwar zuciya ga samun wannan budi.

Wadannan abubuwa guda biyar su ne labule,ko hijabi,da yake kare
zuciya ga barin ganin allon Lauhul Mahafuz wanda yake kunshe da dukkan
ilmai na gaibu.Kasar da wannan labule kuma ya dogara ga aikin mutum.
Wanda ya shagala da ibada,ya tsarkake zuciyarsa ta hanyar barin sabo
da bin sha'awe-sha'awen zuciya,sai a yaye masa hijabin.Da an yaye wa
mutum wanan hijabi,sai ilmin gaibu ya yi ta kwarara cikin zuciyarsa,
hakikanin abubuwa ya budu ga fahimtarsa,kuma ya san Allah sani na
yakini.

Wannan shi ne hakikanin abinda suke nufi da YAYE HIJABI.Kuma
mai karatu zai lura cewa shi wannan sani,ko MA'ARIFA,da suke zancensa
abu ne bako a Musulunci, ba shi da tushe a cikin littafin Allah ko
hadisan Annabinsa, sai dai Sufaye sun samo shi daga ra'ayoyi,
falsafofi da tunane-tunane da suka aro daga al'ummai da addinai
dabam-daban.

Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 21 Insha Allah.

Abu Aisha journalist.
Jibwis Social Media Katsina.

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve