Thursday, 3 August 2017

So kuke a barwa wasu Abujar?

So kuke a barwa wasu Abujar?

Biyo bayan sanarwar da kungiyar Izala ta kasa tayi na gayyatar jamaa su shaidi bude sabon masaukin baki mallakin ta (Sheikh Abubakar Mahmud Gumi Guest House), sai naga wasu na kumfar baki wai yaya zaayi masaukin baki a Abuja? mai yakai addini Abuja? Da ma asibiti akayi da Kudin, me yasa ba'a kai kudin ga IDPs ba? Wasu kuma me yasa baa saka sunan Sheikh Jaafar ba?

Ni kuma nace:
  Da farko dai duk wanda yake ganin mai dace a ce Izala na da masauki a Abuja ba to ya bayyana jahilci da  kauyancin sa a fili.

Ana yawan yin waazi a Abujar nan, ko ita Abuja Allah bai ce ayi mata waazi ba? Bakasan Sheikh Usman Dan Fodio har gaba da Abuja yakai sakon Allah ba?

To so kuke kullum aka je waazi a Abuja sai dai a sauka A hotels ku samu kofar sharri da yarfe ga bayin Allah? Ko so kuke suke kwana a kan titi arnan Abujan suce ga wasu 'yan ta'adda sun shigo gari? Ko so kuke mu fice daga Abujar mu bar wa masu cewa Allah uku ne suyi ta kafirci a ciki ana zagin Allah da manzon sa? Ko kun dauka shi addinin a iya Sokoto ko kano ko Borno ne akace ayi shi? Ya kamata aje Makaranta ayi karatu ko zaa waye.

Maganar yin asibiti ga musulmai  wanna hakki ne  akan kowane musulmi ba wai kungiyar Izala kawai ba, kaima idan ka ginawa musulman ai kayi kokari kuma kayi jihadi kuma Allah zai baka lada idan yaga dama, ko cewa akayi dole sai Izala ce zata gina muku asibiti ku me kukeyi?

Masu cewa kuma an bude wannan gida ne domin alfasha su kuma su da Allah zasuyiwa masa  bayani dalla dalla a ranar Alqiyama.

Yan uwa masu nuna damuwa akan me yasa ba'a sakawa Sheikh Ja'afar su na ba ya kamata ku sani, Sheikh Ja'afar darajar sa a kungiyar Izala ta wuce inda kuke tunani saboda dan wannan kungiya ne tun yana jan baki a kungiyar har Allah yasa yaje yayi karatu ya dawo yana waazi da karantarwa a wannan kungiya.

Kafin a gina wannan gida a sakawa Shugaba Mai Gandu Muhammad da Sheikh Ismail Idriss da Sheikh Abubakar Imam Ikara da A.A Tofa su na Izala ta sakawa kadarorin ta sunan Sheikh baban Saalim su na a gurare da yawa, Lokacin da Allah ya karbi rayuwar Malam take Shugaban  Izalar jihar Kano  Sheikh Dr Abdullahi Saleh Usman Pakistan ya sakawa babban masallacinsa sunan Sheikh Jaafar Mahmoud Adam, Babban dakin taro na kungiyar Izala dake masallacin Izala na Gwallaga dake Bauchi sunan sa Sheikh Jaafar Mahmoud Adam Conference Hall.

Yan gudun hijira kuwa Izala ta tura musu tallafin kayan abinci da sutura na kimanin miliyan ashirin da biyar 25,000,000 wanda ni Ismail shaida ne. Alhamdulillah kai da kake wannan maganar  me ka tura musu tsakanin ka Allah?  Ko kai ba yan uwanka bane? Ko kai baka son ladan?  Ko Izala ce kadai ke da hakkin taimaka musu?

Muna fatan Allah ya taimaki jagororin Izala Sheikh Bala Lau, Sheikh Dr Ibrahim Jalo Jalingo, Engr Mustapha Imam Sitti. Allah ya kara musu ikhlasi damu baki daya. Allah ya sa mu gama da duniya Lafiya ya hada mu a Alannar Firdausi don rahamar sa.

Isma'il Maiduguri
10 Dhul Qa'da 1438
03/Aug/2017

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve