FITOWA TA 2
Daga Littafin:-SUFANCI DA AKIDUN SUFAYE.
Jerin Littafan Sufanci Na 1.
Wallafar:-Prof.Umar Labdo(hafizahullah).
Yadawa:-www.jibwiskatsina.blogspot.com
Ci gaba------->
Da farko dai yana da kyau mu nemo asalin kalmar Sufi ,ko kuma
assufiyyu,watau mai yin sufanci,domin daga ita ne aka samo Kalmar
tasawwuf,watau sufanci.
Akwai wasu malamai dake ganin cewa Kalmar Sufi ta samo asali ne daga
Kalmar Girkanci da ake cewa sofiya,watau hikima.Dalilin da irin
wadannan malamai ke bayarwa kan ra'ayinsu shine,duk inda ka ga Sufi,to
zaka iske shi mutum ne mai hikima,mai yawan tunani akan hikimomi da
mamake-mamaken halittun Ubangiji.
Wadansu kuma suna ganin cewa Kalmar ta samo asali ne daga suffa.Shi
suffa wani wuri ne a masallacin Annabi (s a.w) a Madina inda matalauta
daga cikin Sahabbai,wadanda ba sa saye ba sa sayarwa sai ibada,suke
zama a cikinsa. A wajen masu wannan ra'ayi,manyan Sahabbai masu zama a
wannan wuri da ake Kira suffa su ne asalin Sufaye,kuma daga sunan
wurin kalmar Sufi ta samo asalinta.
Wasu malaman kuwa cewa suka yi ita wannan kalma ta samo asali ne daga
sunan wata kabilar Larabawa da ake kira Banu Sufa.Wannan Kabila ta
shahara da rikon addini da tsoron Allah,don haka ake ganin cewa su ne
asalin Sufaye.
Zamu dakata ana sai fitowa ta 3 Insha Allah.
Abu Aisha Journalist Bmj.
Jibwis Social Media Katsina
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve