Friday, 10 March 2017

SHIN MENENE AGAJI? KUMA MENENE AIKIN 'YAN AGAJIN IZALA?



Abdullahi I. N. Bakori (Director Katsina State)

Da farko masu karatu muna so ku gane aikin
'yan agajin Izalatul Bidi'ah wa iqamatis Sunnah
a cikin Al'ummah.

Abun da ake nufi da Agaji shi ne taimako, idanan ce Dan Agaji, to wani mutum ne wanda ya
sadaukar da rayuwarsa domin ya taimakawa
dukkan wanda ke bukatar taimako.
Sannan dole ya zama mai iya Agajin ba wanda
za a Agaza masa ba. Dan Agaji ya na taimakawa
wanda hadari ya rutsa da shi wajen ba shi
taimakon farko wanda a turance ake cewa (First
Aid) wannan hadari na jirgi ne ko mota ko
babur ko keke da sauransu, sai kuma abin da
ya shafi gobara, annoba, ambaliyar ruwa da
makamantansu.
To a irin wannan lokaci Dan Agaji Zai bada
taimakon farko kafin akai majinyaci asibiti ta
hanyar tsaida jinin dake zuba daga rauni, a
tsaftace wajen, sannan a daure da kyalle mai
kyau don hana shigar wata cutar daban.
Baya ga haka kuma Yana daga cikin aikin 'yan
agaji idan za a yi wa’azi ko wani taro na addini,
dan agaji ne ke fara zuwa wajen don gudanar
da shirye-shirye wajen saukaka cunkoso ga
jama’ar da za su zo a yayin taron, Sannan a
samar da tsaro tare da daidaita kayayyakin
wa’azi, samar da haske, kayan sauti da
sauransu.

Ire-iren wadannan bukatu kungiyar Izala ta ga
dacewar kirkiro rundunar Agaji da za ta yi aiki
tukuru tun fiye da shekaru 30 da suka gabata.
Tun lokacin wannan runduna ta fara gudanar da
ayyukanta, sannan kuma ta ke kokarin inganta
tsare-tsarenta a kullum don dacewa da
kunkiyoyin duniya daban-daban kamar yadda
ake gani a yau.
Rundunar agajin Izala ayyukanta a tsare suke
kamar yadda na bayyana cewa idan hatsari ya
rutsa da mutum ko wane iri ne mu kan jajirce
mu taimaka, sannan a lokacin aikin Hajji zaka ga
'yan agaji a sansanonin alhazai su na taimakawa
a yayin tafiya kasa mai tsarki da kuma dawowa.
Don haka zaka ga al’umma ne daban-daban
suke taruwa a filayen tashi da saukar jiragen
sama, wasu daga kauyuka suka fito ba su san
ko ina ba, don haka ‘yan Agaji za su taimaka
musu wajen nuna musu yadda za su yi har a
cimma nasara. Sannan shi ma wayayye akwai
fannonin da za a taimaka masa a sansanin kafin
ya tashi zuwa kasa Mai Tsarki.
Majalisar Agajin Izala tana Tafiyane karkashin
doka, wadda bata sabawa shari'a ba, yana daga
cikin Dokar agaji, wajibi ne idan ana gudanar da
wani taro wanda yake halastacce na addini
Wadda Uwar Kungiya Ta shirya dan Agaji ya je
ya taimaka ya bada gudumawarsa . Kuma
dukkan wani taro da addini bai yarda da shi ba
ko da an danganta shi da addini to a wajen dan
Agajin Izala haramun ne ya halarci taron.
Majalisar agaji tana Gayyato Hukumar 'Yan
Sanda (Police), Hukumar Kiyaye Hadura (Road
Safety), Hukumar Bada Agajin Gaggawa (NEMA),
Hukumar Kashe Gobara (Fire Service), Hukumar
kiyaye Sha da fataucin Miyagun Kwayoyi
(N.D.L.E), Jami'an Kula da Lafiya (Health),
Malaman Addini Masu Wa'azi, inda kowa Zai zo
ya Karantar da yan Agajin Irin Gudunmawar da
Dan Agaji Zai bada Yayin da ake Neman
Taimakon Gaggawa a dukkan wadannan Fannoni
da muka Zayyana Muku a sama, Domin Aikin
Agaji abu ne da yake son a yawaita Muraja'ar sa
lokaci bayan lokaci.
Dan haka 'Yan agajin Izala aikin su a bayyane
yake a fili, kuma Gwamnati da jami'an tsaro sun
san wannan tun fil azal.

1 comment:

Your Comment will help us to improve