Friday, 18 November 2016

LABARAI A TAKAICE


*Shugaban Naijeriya Muhammadu Buhari a yammacin jiya ya dawo daga birnin Marrakech na kasar Morocco, bayan halartar taron Majalisar Dinkin Duniya kan Sauyin Yanayi.

*Taron lafiyar muhalli da a ka gudanar a Morocco zai iya zama riba ga Najeriya don yadda shugaba Buhari ya tafi taron da bayanan hanyoyin tsabtace malalar gurbataccen mai a yankin Ogoni da kuma farfado da tafkin Chadi.

*Kasashen Afurka da ke kudu da yankin Sahel na kara daukar matakai don matsa lamba ga manyan kasashen duniya masu gurbata yanayi da hayakin masana'antu, su tallafawa kasashe masu tasowa da kudin aikin kare kai daga dumamar yanayi.

*Goni Ahmed shine shugaban hukumar kare muhalli na Najeriya.Ya ce sun tafi da tsari mai kyau taron na Morocco da hakan zai tallafawa Najeriya ga kare muhallin.

*Masana lamuran kare muhalli na ganin tarukan za su tasiri musamman wanda a ka fara a birnin Paris da ya kawo jituwar kasashen kusan 170 don aiki tare ga kare lafiyar muhalli.

*Babban abun da kan lalata muhalli a Najeriya shine sare bishiyoyi don iccen girki, da ya zama mai muhimmanci a bullo da wassu hanyoyin zamani don kare dazuka.

*Mataimakin babban Sakataren watsa labaran jam'iyyar APC TIMI FRANK ya maida wa gwamnan jihar Kaduna martani akan cecekucen da sukeyi tsakaninsa da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.

*"El-Rufai baiyi komai ba a jihar Kaduna tun da ya hau gwamnati a jihar Kaduna amma ya tattara karfinsa kaf yana yi ma Atiku rashin kunya wanda ba sa'ansa bane."

*Yayi kira ga El-Rufai da ya dai na saka shugaban kasa Muhammadu BUHARi a cikin fa'darsa domin Atiku ya na daga cikin wadanda suka yi ma Buhari aiki tukuru domin nasara sa a zaben da ya gabata.

*Shirye-shirye sun yi nisa kan zaben shugaban kasar Ghana ranar 7 ga watan gobe.
'Yan takara sun dage da kamfen don wannan zabe da 'yan adawa za su fafata da shugaban da ke kan gado John Mahama.

*Mahama dai ya gaji kujerar daga marigayi John Atta Mills inda a yanzu ya ke neman tazarce.

Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
18/November/2016
18/Safar/1438

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve