Thursday, 17 November 2016

LABARAI A TAKAICE


*Daya daga cikin lauyoyin dake karre kanal Sambo Dasuki Malam Lawal Raji yace maganar nan ta cewa wai an yiwa dasuki tayin zuwa ya ziyarci mahaifinshi harma wai  ya halarci jana'izar shi ba gaskiya bane.

*Lauyan yace da a ce anyi hakan to tilas shi a matsayin lauyanshi sai ya san da haka saboda haka tsarin shari'a ya zayyana.

*Lauyan yace maganar kawai gwamnati ta shirya ganin kotuna har guda uku sun bayar da belin shi Dasukin amma gwamnati tana ci gaba da tsare shi.

*A yau Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan Zai Kawo Ziyarar Gaisuwar Ta'azziya A Sokoto

*Jonathan tare da rakiyar tsohon gwamnan Attahiru Bafarawa, wasu gwamnonin da tsoffafin ministoci za su sauka da karfe 12:30 na rana a filin jirgin saman Sokoto, daga nan sai su ziyarci Sarkin Musulmi don yi masa gaisuwa.

*Za a yi Sallah da cin abincin rana a gidan Garkuwan Sokoto tare da bakin da suka zo.

*Tsohon Gwamnan Jihar Abia, Orji Kalu Ya Sauya Sheka Zuwa APC,
Shugaban jam'iyyar APC, John Oyegun da sauran masu rike da mukaman jam'iyyar ne suka tarbi Orji Kalu da sauran tawagarsa a hedikwatar jam'iyyar dake Abuja.

*Kungiyar "National Association of Nigerian Students dake Uganda, suna kira ga Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da kuma Babban Bankin Kasa (Wato Central Bank of Nigeria). Akan a dubi halin tsadar rayuwa da da 'yan asalin Nijeriya dake karatu a kasashen waje suke ciki dalilin zoben da aka sanyawa katin ATM din duk wanda ke wajen Nijeriya.

*Rundunar 'yan sandan Najeriya ta nuna hotunan wadanda ta kama da zargin gungun masu sace mutane ne.

*Cikin mutanen har da wani da ke sanye da kayan Sarki na sojan gona na soja. Rundunar dai a baya-bayan nan ta damke masu sace mutane da dama ciki har da a tsakiyar yankin arewa musamman tsakanin Abuja da Kaduna.

*Idan Da Ni Ne Shugaban Kasa, Da Boko Haram Ba Za Ta Yi Tasiri Ba, Inji Tsohon mataimakin shugaban Naijeriya Atiku Abubakar

Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
17/Safar/1438
17/November/2016

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve