Tuesday, 15 November 2016

LABARAI A TAKAICE


*Hukumar alhazan Najeriya NAHCON ta isa Birnin Gombe yau Talata domin duba aiyukan ofisoshin alhazan jihar da mu su lasisin aiki da hakan zai kara inganta kula da jin dadin alhazai.

*Hukumar dai za ta ba da lasisi mai matakai 3 A B C da hakan zai nuna fifiko wajen rabiyar kujerun alhazai a aikin hajji mai zuwa na 2017.

*'Yan kungiyar Shi'a mabiya Ibrahim Elzakzaky sun yi arangama da 'yan sanda a Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya.

*'Yan Shi'an dai na tattaki ne da su ka saba  duk shekara daga Kano zuwa helkwatar su a Zaria.

*Rahotanni sun nuna 'yan Shi'an sun wabci bindigar wani dan sandan kwantar da tarzoma inda su ka harbe shi da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar sa.

*Daga nan 'yan shi'an su ka yi awun gaba da bindigar kirar AK 47

*Jami'an 'yan sanda sun bi su inda hakan ya haddasa musayar wuta tsakanin sassan biyu da wani dan kungiyar Shi'a ya rasa ran sa.
Wassu rahotanni na nuna wadanda su ka rasa ran su ka iya kai wa 5-10.

*Tsohon ministan jirage na Najeriya Femi Kayode na ci gaba da kasance a tsare a gidan yarin Kuje da hakan ya shafi ci gaba da shari'ar sa kan tuhumar almundahana a babban kotun tarayyar Najeriya da ke Lagos.

*Ban Ce Zan Marawa Atiku Baya A Zaben 2019 Ba, Kawai Abinda Na Ce Shine Atiku Tamkar Uba Yake A Wajena, Inji Gwamna Bindow Na Jihar Adamawa.

*Yau Talata Kungiyoyi Daban-daban Za Su Gudanar Da Zanga-zangar Nuna Rashin Bukatar Majalisa A Nijeriya

*Kungiyar ISMOG ita ma tana daga cikin kungiyoyin da za su gabatar da zanga -zanga a Majalisar wakilan Nijeriya da ta dattawa a yauTalata sha biyar ga wannan wata.

*Wannan zanga-zanga za'a yi ta ne domin neman 'yanci dangane da badakalar dake faruwa a Majalisa da kuma nunawa duniya ra'ayin kungiyoyin na rashin bukatar Majalisa a Nijeriya.

*An gargadi dalibai 'yan asalin jihar Kano su guji zuwa gidaje Rediyo su na tozarta manufofin gwamnati, musamman da su ka shafi harkokin na ilimi.

Gwamna Abdulahi Umar Ganduje na barazanar hana irin wadannan dalibai kudaden alawus na karatu.

*Allah ya yi wa Mai alfarma tsohon Sarkin Musulmi na 18 a daular Usmaniyya da ke Najeriya Alhaji Ibrahim Dasuki rasuwa.

*Marigayi Ibrahim Dasuki ya rasu ne jiya Litinin da daddare a wani asibiti da ke birnin Abuja yana mai shekara 93.

*Wata majiya a fadar Sarkin Musulmi da ke Sakkwato ta shaida mana cewa tuni aka fara shirye-shiryen jana'izarsa kuma ana sa ran gudanar da ita da misalin karfe 2:00 na yau talata a birnin na Sakkwato.

*Alhaji Ibrahim Dasuki, wanda shi ne mahaifin tsohon mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan al'amuran tsaro, Kanar Sambo Dasuki, ya rasu ya bar 'ya'ya da jikoki da dama

*Marigayi Ibrahim Dasuki ya zama Sarkin Musulmi ne a watan Disambar shekara ta 1988 bayan rasuwar Sarkin Musulmi na 17 Alhaji Abubakar Sadik na 3.
Ya kwashe shekaru takwas kan mulki kafin gwamnatin soji ta Marigayi Janar Sani Abacha ta sauke shi a shekara ta 1996.

Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
15/Safar/1438
15/November/2016

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve