*Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya nada mai shari'a Jostis Walter Nkanu Onneghen a matsayin mukaddashin babban alkalin Najeriya.
*Onneghen dai ya zama mukaddashin babban alkalin ne biyo bayan ritayar babban alkali Mahmud Muhammad wanda ya yi ritaya bayan cika shekara 70 a duniya.
*Babban alkali dai a Najeriya shine shugaban hukumar kula da lamuran shari'a na kasar NJC.
*Hukumar lafiya matakin farko ta babban birnin Najeriya Abuja ta yi gangamin ilmantar da Fulani makiyaya muhimmancin rigakafin cutar shan inna mai gurgunta yara ko ma sanadiyyar mutuwar su.
*Babban sakataren hukumar lafiyar Dr.Rilwanu Muhammad ya ja hankalin Fulanin muhimmancin ba da hadin kai wajen rigakafin don samun nasarar kawar da cutar daga Najeriya.
*Sarkin Jiwa a yankin Abuja Alh.Idris Musa na daga iyayen kasa da su ka shaida taron don karfafwa Fulani guiwar kan rigakafin.
*Shan inna dai ta sake bulla a yankunan arewa maso gabashin Najeriya da ke farfadowa daga illar Boko Haram.
*'Yan takara 7 ne za su fafata a zaben shugabancin Ghana da za a gudanar ranar 7 ga watan gobe.
*Cikin 'yan takarar har da shugaban da ke kan gado John Mahama da kuma wani dan takara da ya tsaya ba tare da jam'iyya ba da a ke kira "INDIFENDA "
*Ghana dai na daga kasashen Afurka ta yamma da ke tinkaho da ci gaban mulkin dimokradiyya inda gwamnati mai mulki kan iya shan kaye a zabe.
*Amurkawa da dama sun fantsama kan manyan titunan wassu biranen kasar don nuna fushin su ga nasarar Donald Trump a zaben shugaban kasar.
*Amurkawan dai na daga cikin wadanda ke ganin Trump ba shi da manufa mai kyau.
*Shugaba Barack Obama mai barin gado ya gaiyaci Trump fadar White House don tattaunawa da daukar alwashin shirin mika ragamar mulki lami lafiya.
*Allah ya yi wa Shahararren Malamin addinin Musulunci na Kaduna, Sheik Muhammadu Sanusi Gumbi rasuwa a daren jiya.
*Malam Sanusi Gumbi ya yi jinya na dan lokaci, inda ya rasu a babban birnin tarayya Abuja. Kuma ana sa ran jana'izarsa a yau Juma'a da karfe daya na rana a Massalacin Sultan Bello dake garin Kaduna. Allah Ya jikansa da rahama.
Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
11/Safar/1438
11/November/2016
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve