*A jiya Laraba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari kan kisan da aka yi a jihar a ranar Talatar da ta gabata.
*Ganawar wabda aka gudanar a fadar shugaban kasa dake Villa Abuja, ta kai tsawon mituna 40.
Idan ba a mance ba, a ranar Talatar da ta gabata wasu 'yan bindiga sun kai hari kan wasu masu hakar zinari a wani kauye da ake kira Bindin dake jihar Zamfara, inda suka kashe mutane kusan 36.
*Karar Bindiga Ta Sa Wani Fasinja Ya Yanke Jiki Ya Fadi A Yayin Da Sojoji Suke Atisaye A Filin Jirgin Sama Na Murtala Dake Jihar
Lagos
*Rahotanni sun nuna cewa duk da sanarwar da hukumar gudanarwa ta filin jirgin saman ta bayar kafin sojojin saman su soma gudanar da atisayen, hakan bai hana daya daga cikin fasinjojin dake tahsar jikin yanke jiki ya fadi ba a lokacin da ya dinga jin karar luguden wutan da sojojin suke yi.
*Sojojin sun gudanar da atisayen ne a ranar Larabar da ta gabata mai taken yaki da ta'ddanci.
*Shugaban rundunar sojojin kasa, Janar Tukur Yusuf Buratai ya musanta jita-jitar da wasu kakafafun yada labarai ke ta yadawa na cewa ya daura laifin mutuwar su Kanal Abu Ali kan shugaban kasa Muhammadu Buhari.
*Mai magana da yawun rundunar sojoji, Kanal Sani Kukasheka Usman, ya bayyana cewa babu kanshin gaskiya a labarin, don haka kada jama'a su yarda da wannan rahoto na bogi.
*Kasashen duniya na ci gaba da taya murna ko maida martani kan nasarar da Donald Trump ya samu na lashe zaben Amurka. Da yawa dai kasashe sun yi dari-dari da takarar Trump saboda kalaman nuna kin jinin baki da ya ke yi.
*Tuni dai bisa al'ada gwamnatin Najeriya ta taya Trump murna da fatar aiki tare da shi ga wanzar da huldar da ta yi karfi tsakanin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da shugaban Amurka mai barin gado Barack Obama.
*Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya kaucewa irin jawaban da ya saba lokacin kamfen na nuna tsaurin ra'ayi kan baki da musulmi;inda ya ce zai yi aiki da kowa don ci gaban dimokradiyya.
*Trump ya nuna kowa ya mara ma sa baya daga dukkan bangarorin jinsi da addinai. Hatta wadanda ba su mara ma sa baya ba,Trump ya yi kira gare su, su ba shi hadin kai don aiki tare.
*Hillary Clinton ta jam'iyyar Democrats da ta sha kaye ta yi jawabin amsar kaddarar da ta faru da nuna "Gaba ta fi baya yawa"
*Hillary da ke tare da mijin ta tsohon shugaban Amurka Bill Clinton, ta nuna godiya ga wadanda su ka mara ma ta baya da cewa duk da ba haka su ka so sakamakon ya kasance ba amma wata rana wani zai bullo samun nasarar canjin da a ke bukata.
Hillary ta ce ta taya Trump murna da zuciya daya da kuma fatar ya samu nasarar shugabancin Amurka.
Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
10/Safar/1438
10/November/2016
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve