Sunday, 16 October 2016

Kungiyan Izala Da Kai Jama'a Aiki Makka?


Daga: Mahmud Isa Yola

Yana da kyau idan mutum zai magana ya kasance mai adalci. Musamman ma idan kana magana akan abunda ya shafi addini, sai dai ba kowa bane yake da tunani da zai iya yin hakan.
Na ga rubutu da yake yawo a kafar sadarwa ta FaceBook cewa kungiyan Izala tare da gwamnatin Nijeriya ta dau wasu mata ta shilla da su kasar Saudiyya da nufin aiki a Harami amma aka kai su bayan gari. Na yi mamakin yanda kafafen yada labarai suka zama tamkar tolotolo wanda in ya ji abu zai amsa ba tare da ya bincika ba. Wannan karya ne! Ga gaskiyar lamarin nan:
Kungiyan Izala ta wallafa shafukan ta cewa tana tallan sabon jami'a da Kasar Saudiyya ta bude karkashin jagorancin Sheikh Imam Abdurrahman Sudais. Ita kungiyar Izala ba tace tana da hanya da za ta bi wajen tura dalibai wannan makarantar bane. Yanda sanarwan yazo haka ta yada shi saboda sanar da daliban ilimi.
Abu na biyu kuma shine sanarwa da kungiyar ta yi karkashin tsarin ta na sama wa mutane aiki. Kungiyar ta sanar karkashin wani kamfani cewa ana daukar ma'aikata a kasar Saudiyya wadanda za su yi hidima a harami. Mu fahimci cewa kungiyar Izala ba ita ce ke samar da aikin ba, abunda za ta yi shine hanya ga wanda yake bukata. Wannan kuma na daga kudirin kungiyar na sama wa jama'a aiki saboda rage zaman banza.
Babban abunda jama'a ya kamata su sani anan shine, ZUWA YANZU BABU WANI KO WATA WANDA YA TAFI KASAR SAUDIYYA SABODA AIKI DAGA KASAR NAN A KARKASHIN WANNA SHIRIN KODA KUWA A HARAMIN NE BALLE ACE HAR YA KAI GA AN KAI WASU BAYAN GARI.
Ana kan tantancewa da kuma taimaka wa wadanda suke bukatan aikin a karkashin wata kamfani da take bada aiki mai suna "Dialogue". Ita kungiyan Izala kokarin ta shine ta sama wa jama'a hanyan samun aikin bayan ta tabbatar da sahihancin aikin.
Abun da masu kalubalantar kungiyan Izala basu gane ba shine, ita kungiyan izala ba zata daina aikin alkhairi ba saboda hauragayyar su. Kungiyar Izala kuma ba wannan ne karon farko da take sama wa mutane aiki ba.
To amma duk da cewa babu wani mutum koda kwara daya da ya je kasar Saudiyya, sai gashi masu yada karya sun fito suna kalubalantar shirin saboda muradun su na kiyayya ga kungiyar. Kuma kowa ya ga rubutun da kungiyar ta yi na cewa ba ta amince da karbar ko da kwandala ba, amma sai makaryata suka fito suna yayata cewa ai an karbi kudi a hannunsu.
Muna kalubalantar masu wannan rubutu da su kawo mana zahiran hujjoji na yin wannan rubutu. Idan kuma sun gina rubutun nasu ne akan karya, to muna tunatar dasu cewa karya dubu bata karya gaskiya daya.
Allah ya ba mu ikon gane gaskiya gaskiya ce ya ba mu ikon binta.

Mahmud Isa Yola,
National PRO, Jibwis Social Media Nigeria.

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve