Thursday, 13 October 2016

IZALA TA BARRANTA KANTA DA RIKICIN SHI'A

Daga: Jibwis Nigeria

Babu ruwan Izala da rikicin Shi'ah da mutanen gari!
Kawai abin da izala ta fadi shine Ta goyi bayan matakin da gwamnantin jihar Kaduna ta dauka akan ayyukan 'yan Shi'a. Amma rikicin shi'a da mutanen gari wannan bai shafi Izala ba.
Haka zalika Izala Tana kiran mutane da su daina daukan irin wannan hukunci a hannun su, wannan aikin jami'an tsaro ne, kuma aikata irin wannan ta'asa zai zama da zunubi tare da amsa tambaya ranar gobe kiyama. Da fatan za'a bi doka da oda a duk lokacin da irin hakan ya taso.

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve