*FITOWA TA 6.
*Daga Littafin:-AKIDAR YAN SHI'A DANGANE DA SAHABBAI.
*JERIN LITTAFAN SHI'A 1
*WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO(hafizahullah).
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com
Kiyayyar yan shi'a ga Sahabban Annabi(s) ta kai matuka har suka halasta la'antar su. Sun ma dauki la'antar Sahabbai a matsayin ibada wacce suke neman kusanci ga Allah da ita !! Kuma ko a cikin Sahabban ma, kiyayyarsu ta fi tsanani ga shugabanninsu mafifita:Abubakar da Umar. Duba wannan ruwaya, wacce wani malaminsu mai suna Mulla Kazim ya nakalto, yana dangana ta BISA KARYA ga Ali Zainul Abidin binu Hussain binu Ali binu Abi Dalib, Allah ya kara musu yarda. Ya ce:Abu Hamza Althumali ya karbo daga Ali Zainul Abidin Cewa ya Ce,. "Wanda ya la'anci Jibtu da Dagutu (yana nufin Abubakar da Umar) la'ana guda, Allah zai rubuta masa lada dubu sau dubu, ya kankare masa zunubi dubu sau dubu, kuma ya daukaka masa daraja dubu sau dubu saba'in.Kuma wanda ya la'ance su da yammaci la'ana guda, za'a rubuta masa kamar haka. (Mai ruwaya) ya ce:Sai shugabanmu Ali binu Hussaini ya wuce(bayan ya fadi wannan magana, ni kuma) sai na shiga wurin shugabanmu Abu Ja'afar Muhammad Albakir na ce masa:Ya shugabana, wata magana ce na ji daga mahaifinka. Sai ya ce:Fade ta mu ji, ya Thumali. Sai na maimaita masa maganar. Sai ya ce :Haka take, Thumali! Ko kana so in yi maka kari? Sai na ce:E, ya shugabana. Sai ya ce :Wanda ya la'ance su la'ana guda a ko wace safiya ba za'a rubuta masa zunubi ba a wannan wunin har zuwa yammaci, kuma Wanda ya la'ance su la'ana guda da yammaci ba za'a rubuta masa zunubi ba har ya wayi gari.''
(Duba AJMA'UL FALA'IHI na Mulla Kazim, 513).
Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 7 Insha Allah.
Abu Aisha Journalist.
Jibwis Social Media Katsina.
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve