A jiya ne Shugaban JIBWIS na Jihar Katsina
Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina
Ya kar6i bakuncin Kwamishinan Hukumar Za6e ta Jihar Katsina wanda ya samu wakilcin Alh. Aliyu Alkali (Mai Kula da bincike da tsare-tsare na Hukumar) da Alh. Buhari (P.R.O)
Sun kawo ziyarar ne domin sanar da aikin da Hukumar Za6e Ta Kasa (INEC) ta shirya zata gabatar a kowace Warda da rumfunan za6e na Kasar nan daga Litinin 6-11-2018 zuwa 12-11-201. Wannan wani aiki ne da ake kira baje koli kafin lokacin Za6e kamar yadda doka ta tanadar. Wannan shiri an shiyar shi ne domin kar6ar korafe korafe da kuma yin gyare gyare ga dukkan wanda ke da wata matsala akan katin za6en shi.
Da wannan ne Daraktan Da'awa na JIBWIS ta Kasa kuma Shugaban JIBWIS na Jihar Katsina
Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina
Ke kira ga Limamai da Malamai suyi kira da wayar da kai ga al'ummar Musulmai akan wannan aikin da Hukumar Za6en zata gabatar domin aikin zai anfani al’umma. Kuma wannan aikin ba na Limamai da Malamai ba ne kadai ana bukatar duk wanda ya samu wannan sako kuma ya fahimce shi to yayi kokari ya isar da shi zuwa ga yan'uwa kuma yayi kokari ya wayar masu da kai akan wannan aikin da Hukumar Zabe ta shirya zata gabatar kowa ya bada irin tashi gudummuwar domin ganin an cimma nasarar da ake bukata.
GA TSARIN YADDA AIKIN ZAI KASANCE:
1. Za'a kafe sunaye a kowace rumfa. Ana bukatar kowa yaje ya duba sunanshi.
2. Domin ka tabbatar da sunanka da sauran bayanen ka dai-dai suke ba kuskure akan katin ka.
3. Ana bukatar duk rumfar da wani ya mutu idan an ga sunan shi a sanar da ma'aikatan hukumar domin a cire sunan shi.
4. Cire duk wanda ke da shekaru kasa da 18. Domin akwai wadan da anyi masu register shekarun su ba su kai ba.
5. Ko wane Mai Unguwa da 'Yan Unguwa su tabbatar da duk wanda ke cikin sunayen Unguwarsu sun sanshi musamman Kananan Hukumomin da ke kan iyaka da Janhuriyar Niger.
6. Duk wanda yasan yayi register sama da daya (1) yayi kokari ya tabbatar da ya maida ta guda daya.
7. Mutane zasu kai korafe korafen su a Collection Centre dinsu daga Litinin 6 zuwa Litinin 12 November.
8. Za'ayi maganin matsaloli da korafin mutane a ranakun Lahadi 11 da Litinin 12 November, 2018
9. Kar6ar katin Za6e na dindin din. Duk wanda yasan yayi sabon kati daga March, 2017 zuwa March, 2018 katin shi ya fito za'a zo da Katin a kowace Collection Centre daga Litinin 6 zuwa Litinin 12 November, 2018. Daga nan duk wanda bai ansa ba to zai je Ofishin Hukumar INEC din na Karamar Hukumar su.
Amma a akwai Kananan Hukumomi Guda 3 wadan da aka karama kwana 3 wato zuwa 15 November zasu cigaba da kar6a su a nan Ward Collection Centre din su sune: Kankia, Kusada, Ingawa saboda za6en maye gurbin da za'ayi 17 November, 2018
Wannan aiki dai duka za'a gudanar dashi ne a fadin Kasar nan ba wai Jihar Katsina kadai ba.
Muna rokon Allah yayi ma Shugabannin wannan Hukuma Jagoranci da basu ikon yin gaskiya ga wannan babban aikin da ke gabansu ya kuma tsare daga dukkannin makircin masu makirci.
© JIBWIS KATSINA
23 Safar, 1440.Ah
02 November, 2018.Ac
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve