Friday, 17 August 2018

SANARWAR TSARIN IDIN BABBAR SALLAH NA KATSINA

TSARIN SHIRYE – SHIRYEN SALLAR IDI DA WA’AZIN GORON SALLAH NA BABBAR SALLAH TA SHEKARA TA 1439AH./ 2018MD WANDA MAJLISAR MALAMAN KUNGIYAR JIBWIS TA SHIRYA A GARIN KATSINA

Majlisar Malaman Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis – Sunnah tana farin cikin sanar da ‘yan uwa Musulmi cewar:-

1. Idan Allah (S.W.A) ya kai mu Ranar Talata 10 Ga Watan Zhul Hajj, 1439/ 21 August, 2018 za’a gabatar da Sallar Idi kamar yadda aka saba kamar haka:

MASALLACIN JUMA'A NA G.R.A KATSINA

1. Masallacin Idi dake Masallacin Juma’ah na G.R.A, W.T.C Road Katsina da karfe 8:30 na safe in Allah ya yarda.

2. Mai Wa’azi kafin Isowar Liman: Malam Abdurrahim Sabi'u Rafin Dadi

3. Wanda zai Jagoranci Sallar Idi: Malam Safiyyu Al-Kasim Saulawa

2. MASALLACIN JUMA'A NA SHINKAFI

1. Masallacin Idi dake Masallacin Juma'a na Garin Shinkafi, Katsina za'a fara Sallah da karfe 8:30 na safe in Allah ya yarda

2. Mai Wa’azi kafin Isowar Liman: Malam Ahmad Yakubu

3. Wanda zai Jagoranci Sallar Idi: Malam Ibrahim Idris Shinkafi

SANNAN ZA'A GABATAR DA WA'AZIN GORON SALLAH KAMAR HAKA:-

1 RANAR SALLAH

WURI:- Masallacin Rukunin Gidajen Bayajidda Road, G.R.A, Katsina
LOKACI:- Bayan Sallar La’asar
MAI WA’AZI:- Malam Yusuf Shu'aibu
MAI TA’ALIKI:- Malam Bunyaminu Muhammad Balarabe

2 BAYAN SALLAH DA KWANA DAYA

WURI:- Masallacin Sarkin Yaki, Kan Titin One-way, Katsina
LOKACI:- Bayan Sallar La’asar
MAI WA’AZI:- Malam Munir Isah Kerau
MAI TA’ALLIKI:- Malam Abdurrahim Sabi'u Rafin Dadi

3. BAYAN SALLAH DA KWANA  BIYU

WURI:- Masallacin Kiddies Lambun Sarki, Kofar Marusa, Katsina
LOKACI:- Bayan Sallar La’asar
MAI WA’AZI:- Malam Muhammad Usamatu Abbas
MAI TA’ALLIKI:- Malam Safiyyu Al-Kasim Saulawa

Da fatan Allah (SWT) Ya sa mu dace ya karba mana dukkan Ibadar mu kuma ya sanya ayi Hidimomin Sallah lafiya, Amin. Bassalam.

Muhammad Auwal Daura
Sakataren Tsare – tsare.

       ® S.A SOCIAL MEDIA
     JIBWIS KATSINA STATE
               06-12-1439
               17-08-2018

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve