Thursday, 2 August 2018

TAKARDAN BAYAN TARO (COMMUNIQUE) NA TARON KWAMITIN SOCIAL MEDIA NA KASA WANDA YA GUDANA A SAKATARIYAR KUNGIYAR IZALA DAKE BIRNIN ABUJA A RANAR ASABAR 28/07/2018



1. Kwamitin ya gudanar da zama guda biyu: na farko meeting na 'yan kwamiti wanda shugaban kwamiti Alh Ibrahim Baba Suleiman ya jagoranta. Na biyu kuma ganawa da Shugaban kungiyar Izala ta kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau da 'yan majalisar sa.

1. A zama na farko:
*Shugaban kwamitin Ibrahim Baba Suleiman ya jinjinawa dukkan wadanda suka halarci zaman bisa amsa kira a kurarren lokaci, da kuma kokarin da suke yi a jihohin su.

*An gabatar da rahotanni guda uku: (a) na farko rahoton taron (meeting) na National Exco wanda ya gudana a garin Gombe shekarar da ta gabata wanda Muhammad Ahmad Bindawa, mataimakin sakataren kwamitin ya gabatar. (b) na biyu rahoton kwamitin kasafin kudi na uwar kungiya wanda ta zauna a katsina a watan october 2017 wanda Mahmud Isa Yola, sakataren yada labarai na kwamitin ya gabatar (c) rahoton ayyuka wanda Musa H Musa, sakataren tsare-tsare ya gabatar.

3. Shuwagabannin Jihohi sun bada shawarwari akan matsaloli da ake fiskanta wanda wasu a nan take shugaban kwamitin na kasa ya umurci kwamitin sulhu karkashin jagorancin Ustaz Anas Assalafy Fage ta dau mataki.

4. A ganawar Kwamitin da uwar kungiya, Manyan shuwagabanni da malamai da suka halarta sun hada da:

*Sheikh Abdullahi Bala Lau

* Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe

*Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina

*Sheikh Dr. Ibrahim Rijiyar Lemo

*Sheikh Khalid Usman Khalid

*Professor Dauda Ojobi

*Dr. Ibrahim Idris Jos

* Alaramma Ahmad Suleiman Kano

5. Bayan sakataren kungiya na kasa Sheikh Kabir Gombe ya gabatar da abubuwan da taro zai gudana a kan su, Shugaban kungiya Sheikh Bala Lau ya fara da jinjina wa membobin kwamitin inda yace ayyukan da suke yi a kafafen sadarwa a bayyane suke kuma abun yabawa ne. Shugaban ya gargadi membobin kwamitin da su gina aikin su a kan gaskiya saboda gaskiya ita ce matsayar kungiyar. Sheikh Ya kuma yi kira ga membonin kwamitin da su kasance masu warware shubuhohi da wasu suke shigarwa kafafen sadarwa da sunan addini. Sheikh yace membobin kwamitin su kasance masu bincike sosai, su zakulo irin wadannan su rusa su da hujjoji daga Al'Qur'ani da Hadisi. Kazalika shugaban yayi kira ga membobin da su kasance masu wargaza makirce makirce da wasu makiya sunnah suke shiryawa ahusunnah da kungiya a kafafen sadarwa.

6. Sheikh Muhammad Kabir Gombe a nasa bayanan, yayi kira ga membobin kwamitin da su tuna a duk wani abu da zasuyi na rubutu a Social Media cewa su jakadun musulunci ne, saboda haka, duk wani abu da zai amfani musulmai da musulunci da al'ummar kasa dole su goyi bayan sa. Sheikh yace hakika kafafen sadarwa a yanzu sai kara yawaita suke yi, saboda haka suna bukatan wadanda zasu saita tunanin mutane akan gaskiya da addini. Malamin ya gargadi membobin kwamitin da su guji goyan bayan duk wani mutum, ko wata kungiya ko gamayyar mutane dake da manufa da bazai amfani addini ko jama'ar kasa ba.

7. A nasa jawaban, Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina yayi kira ga membobin kwamitin da su wayar wa jama'a kai akan karban katin zabe da yin rijista. Yace kuma yakamata su wayar wa jama'a kai akan alkhairan dake cikin zaban shugaba nagari mai yiwa kasa hidima.

8. Professor Dawud Ojobi  yayi kira ga membobin kwamitin da su kai da'awar addini ga mabiya addinin kirista a social media ta hanyar yin amfani da littafin Bible wanda a cike yake da shari'ar musulunci.

9. Dr. Ibrahim Rijiyar Lemo yayi kira ga membobin kwamitin da su kasance masu gaskiya, kuma masu yada gaskiya a duk inda suke. Yace babu dalilin ragawa wadanda suke cutar da addini ko zagin manzanni ko sahabban su a social media.

10. Shugaban kwamiti Ibrahim Baba Suleiman ya nemi kungiya ta kara wadata membobin kwamitin da kayan aiki. Kuma yayi godiya ga kungiya da ta dauki nauyin zaman da ya gudana kuma ta bada dukkan hadin kai da ya dace.

Sign
Mahmud Isa Yola
National Publicity Secretary, Jibwis Social Media Nigeria.

18/11/1439ah
01/08/2018

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve