Wednesday 20 May 2020

JAWABIN RUFE TAFSIRIN RAMADAN NA WANNAN SHEKARA TA 1441/2020 DAGA SHUGABAN KWAMITIN TAFSIR NA KASA KUMA SHUGABAN JIBWIS NA JIHAR KATSINA - Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina

Daga: Yusuf Hassan Buhari

Da sunan Allah Madaukaki wanda dukkan yabo da godiya sun tabbata a gareshi, bisa ni’imominsa masu yawa garemu. Tsira da aminci su kara tabbata ga Annabi Muhammad (S.A.W) wanda aka aiko da littafi wanda 6arna ba ta zuwa gabanshi ko 6ata, tabbatacciyar hanyar tsira daga dukkan duhu zuwa haske. Allah ya kara aminci ga Alayensa da Sahabbansa za6a66u wanda suka yada wannan addini da dukiyoyinsu da rayukansu. Allah kara tabbatar da mu bisa wannan hanya tasu har zuwa ranar sakamako.

Cikin yaddar Allah (SWT) da ba za’a gabatar da Tafsirai ba a cikin wannan Kasa ta mu saboda kalubalen da aka fuskanta na cutar mashako (Covid 19) da ta bayyana cikin duniya baki daya wanda kafin ta shigo wannan Kasa labari mu ke ji, amma kuma kafin watan Ramadan ta fara shigowa wannan Kasa dan haka ne akai matsaya akan dakatar da tura Malamai masu Tafsir da wannan Kungiya ta sa ba gabatarwa duk Shekara ciki da wajen Kasar nan sanadiyyar matakin da aka dauka na hana taruwar mutane a wuri daya wanda ya kun shi kowa wane irin taro wanda ya shafi Tafsirin ba na. Wand aka ba Malamai damar su gabatar da Tafsiransu da shirye-shirye wanda suka shafi wannan wata na Ramadan da kuma wannan hali da ake ciki a Gida tare da Yan Jarida da ‘Yan Social Media domin su isar zuwa ga sauran al’umma
 
Muna addu’a ga Malaman da suka samu dama su ka gabatar da Tafsirai a gidajensu muna rokon Allah yayi masu sakayya ta alkhairi, abubuwan da su kayi wanda yake daidai Allah ya ba su lada wanda kuma ya ke kuskure Allah ya gafarta ma su. Sauran Malamai kuma da ba su samu damar gabatar da Tafsirin ba muna ba su hakuri muna rokon Allah ya cika ma su ladarsu  duk da ba su samu damar da gabatar da Tafsir din ba a wuraren da aka saba turasu ko a garuruwan da suke. Muna rokon Allah yayi masu sakayya da Jannatul Firdausi

Bayan haka, wannan lokaci da muka kasance bisa ni’imar Allah mun fara Tafsirin wannan  majalisi bisa jarabawar da Allah ya saukar garemu na lalurar wannan annoba ta cutar mashako (Covid 19) wanda ta afkowa duniya tare da sanya firgici cikin rayuwar al’umma.

Muna godiya bisa hadin kai da jama’a suka bayar da biyayya akan umurni da aka bi na hukumomi da masana bisa kokarin dakile wannan cuta ta mashako (Covid 19). Muna rokon Allah ya ba mu lada ya kara karemu daga fadawa cikin wannan jarabawa.

Kamar yadda muka fada muku umurnin da wannan Kungiya ta bayar lokacin bude wannan Tafsiri, wanda yau muke kullewa tare da gabatar da wadannan kiraye- kiraye kamar haka:

1. Muna masu jajantawa ga al’ummar wannan Jiha bisa ibtila’in tashe tashen hankula na 6arayin shanu da kasha-kashen da aka rinka aiwatarwa a wasu sassa na wannan Jiha. Muna masu addu’a ga Allah ya jikan wadan da suka rasa rayukansu a wannan ta’addancin haka muna addu’ar Allah ya maida mafi alkhairi ga wadan da suka rasa dukiyoyinsu yayin wannan jarabawa.

2. Kungiya tayi kira ga jama’a tare da neman su taimaka ma jama’a lokacin da aka kulle jama’a a gidajensu bisa kokarin dakile yaduwar wannan cuta. Mun samu hadin kan jama’a tare da raba tallafin abinci ga mutanen Kananan Hukumomin Daura da Dutsinma.

3. Kamar ko wace shekara Kungiya ta na gabatar da kira wajen tallafawa marayu da gajiyayyu, wanda bisa wannan Kungiya ta sabinta Kwamitin Marayu na Jiha tare da tabbatar da yin aiki tukuru wajen ganin aikin Kwamitin ya kara tasiri cikin bayar da tallafi ga marayu tare da inganta tsarin gudanarwa.

Bayan haka muna kira ga al’umma su taimaka da abinda Allah ya hure masu su kai a Masallatan da ke Unguwarsu domin taimakama marayu da gajiyayyu.

4. Muna kira ga jama’a da su cigaba da bada hadin kai wajen bin shawarwari, dokoki da ka’idojin da Malaman lafiya su ke  badawa ga me da samun kariya ga wannan cuta 

5. Haka kuma muna kira ga Hukumomi da Jami’an tsaro wajen yin aiki tukuru domin magance wannan cuta da kuma ta’addancin da ake fama da shi a wannan Jiha ta mu. Muna kira ga wadan da aka daura ma nauyin wannan ayyuka mu samman na samar da tsaro da su dinga sanya ido suna bibiya domin tabbatar da ana aikin. Haka kuma wadan da ake ba tallafi su kaima al’umma na wannan cuta su ma a sanya ido, a tabbatar da tallafin na kaiwa in da ake bukata. Idan Shugabannin suka tsare hakan su ma Allah zai tsare su.

Daga karshe muna kara ba da hakuri ga yan’uwa bisa rashin tura Malamai ma su Tafsir da akai a wannan Shekara saboda yana yin da muka tsinci kan mu ciki. Su ma Manyan Maluman da aka saba turawa ciki da wajen Kasar nan domin zuwa gabatar da Tafsir muna ba su hakuri bisa rashin samun gabatar da Tafsir sakamakon halin da ake ciki.

Muna rokon Allah ya ansa mana ayyukanmu  da mu kayi a cikin wannan wata na Ramadan ya kuma yi mana baiwa da samun lada akan ayyukan da mu keyi wannan karon ba mu samu damar yi ba. Allah yayi mana jagora yaba mu zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Wassalamu Alaikum Wa Rahamatullahi Wa Barakatuhu

Naku a Musulunci
Sheikh Yakubu Musa Hassan
Shugaban Kwamitin Tafsir na Kasa 
Shugaban JIBWIS na Jihar Katsina
27 Ramadan, 1441
      20 May, 2020

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve