Friday 24 April 2020

ANYI KIRA GA 'YAN SOCIAL MEDIA DA SU KIYAYE: HARSHEN SU, HANNUWAN SU DA IDANUWAN SU


A KODA YAUSHE, ALOKACIN DA SUKE DUBA WAYAR HANNUN SU.

Daga: Shehu A.A.Gashua
          Via
Ibrahim Baba Suleiman

 Harshe yana da Tasiri kwarai da gaske , illa iyaka mu kiyaye shi yayin furta magana mai kyau ko maras kyau.

  Mu guji muggan maganganu a lokacin rubutun ta wannan kafa akan Malamai,Shugabannin mulki da sauran Abokan Aikin mu.

 Mu daina cin mutuncin mutane sakamakon rashin jituwar mu da su na Banbancin Siyasa,Bangaren Addini,Bangaren kungiyoyin mu da sauran su.

  Kada mu yarda hannuwan mu su rubuta karya,kazafi,munafurci da sauran su. Mu tuna fa lalle ne muna tare da mala'ikun Allah masu daukar dukkan lamuran mu masu kyau ko akasin hakan.

 Lalle ne muyi hattara da hotun batsa dake cikin wannan kafa dake shugomana ba tare da sanin mu ba. Idanuwan mu kada su kasance masu leke leken banza domin ganin mugun abu.

 Allahu Akhbar, Allah ya shigo damu cikin watan Ramadan, wata mai Albarka watan da Allah yake ninka ladan Ayyukan bayin sa. Lalle mu kasance masu Rubuta,fadin,ganin Alkhairi a lokutan Ayyukan mu ta wannan kafa.

 Mu kasance musu biyayya da taka tsantsan a koda yaushe wajen bin dokokin wannan Aikin na Social Media. Allah ya yi mana Jagora.

Naku: Shehu A. Abdurrahman Gashua
National photo Editor
Jibwis Social media Nigeria

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve