Wednesday, 13 December 2017

WANENE SHEIKH ABDULLAHI BALA LAU?

Sheikh Abdullahi Bala Lau, Shine Shugaban Kungiyar IZALA Mai Rijista daga Gwamnatin Tarayyar Naijeriya. Wanda kuma kasashen Duniya suka gamsu da tsarin tafiyar kungiyar da yake jagoranta ta IZALA a jerin manyan Kungiyoyin Ahlussunnah Na Duniya.

Ita kanta Majalisar Musulunci ta Duniya (RABI'DA) takan tuntube shi a wasu muhimman Lamuranta da suka shafi musulunci a yankin Afurka, Majalisar ta taso da Shugabanta Sheikh At-turki da 'Yan majalisar Sa takanas ta Kano  sukazo taron da IZALA ta shirya a Abuja, Wanda har shugaban Naijeriya Muhammadu Buhari da sauran jami'an gwamnati suka halarta tare da jiga jigan Maluman Ahlussunnah daga sassan Duniya.

Sheikh Bala Lau mutum ne mai Dattaku, Wanda baya cin mutuncin kowa, sannan yace duk Wanda yaci masa mutunci ya yafe masa. Yace aikin IZALA shine Wa'azi, kuma duk mai Wa'azi Na gaskiya yana tare da suka, haka tarihi ya nuna, Dan haka Malamai suci gaba da Wa'azi su bar masu suka suyi ta suka har wataran da kansu zasu soke.

Shehin Malamin Yana Wa'azi a harcen Larabci, Hausa, Turanci, da fulatanci, Sannan baya da girman kai ko kadan, yana Alaka da kowa a mutunce, yakan dauki shawarwari daga duk wani Wanda ya bashi ingantacciyar shawara.

Ta yaya Wanda ya hada wannan Nasarorin a Dan kankanin Lokaci Na Shugabannin Sa ba zai samu masu masa Hassada ba?

Akaramakallah Hassada, gaba da sauran cin mutunci yanzu aka Fara maka, indai da Nasara, to da kalubale.....

Wannan shine amsar Tambayar wanene Sheikh Abdullahi Bala Lau.

Wannan sako ne daga kwamitin JIBWIS Social Media ta kasa.

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve