SAKAMAKON TARON KWAMITIN JIBWIS SOCIAL MEDIA NA KASA DA WAKILAN KWAMITIN A DUKKAN MATAKAI WANDA YA GUDANA A KONTAGORA DAREN LAHADI 03/12/2017.
Zaman taron wanda aka dauki wajen Awa daya da rabi anayi an farashi da misalin karfe biyu na dare (2:00AM) bayan an tashi wa'azin dare a masaukin 'yan kwamitin.
Babban magatakardan kwamitin na kasa Alh. Adamu Attahiru Kebbi da Babban mai bincike na kwamitin Ustaz Aliyu Ibrahim Kwara ne suka jagoranci zaman.
Tunda farko Shugaban kwamitin a jihar Neja Ustaz Usman Sa'ad ne yayi jawabin maraba da baki a madadin 'yan kwamitin jihar ta Neja.
A nashi jawabin, Shugaban taron Alh. Adamu Attahiru Kebbi ya gabatar da dalilan da suka sanya aka kira wannan taro, sune don a tabbatar da sanayya da kuma kara inganta alaka tsakanin mambobin kwamitin.
Ya kara da yin albishir ga 'yan kwamitin akan matakan da Shugaba Abdullahi Bala Lau yake shirin dauka domin karawa kwamitin kwarin guiwa wajen samarda kayan aiki ga kwamitin na kasa, da kuma koyarda 'yan kwamitin wasu ayyuka na musamman.
Zaman yayi tasiri kwarai da gaske inda aka cinma matsaya masu yawa wadanda suka hada da:
* Anja hankalin 'yan kwamitin akan su cigaba da tsarkake niyya tareda sanya Ikhlasi a dukkan ayyukansu domin gujewa yin aikin banza.
* An kara jan hankali sosai akan ladabi da biyayya ga shugabanni a tsakanin membobin kwamitin cikin abinda ba sabon Allah bane.
* Anyi kira ga Membonin kwamitin akan tabbatar da isnadin labari da ingancinsa tare da bibiyar dukkan bangarori kafin su yada shi.
* Anyi kira ga 'yan kwamitin akan su mallaki Riga da Katin Shaidar zama mambobin kwamitin domin gujewa samun Tirjiya daga jami'an tsaron Kungiya musamman a wajen taruka.
* Anyi Kira ga 'yan kwamitin akan su Rinka sanya abubuwan da suka shafi Kungiya a shafukan Jihohinsu masu daukeda sunan JIBWIS kafin su sanya shi akan Timeline dinsu.
* Anyi ittifaki cewa mambobin kwamitin a dukkan matakai zasu taimaka wajen rufe shafukan BOGI masu daukeda sunan JIBWIS.
*An kara tabbatar da cewa dukkan abinda daya shafi kungiya a matakin Kasa, babban Shafin "Jibwis Nigeria" ne kadai ke da alhakin yadashi kafin kowa.
* Anyi Kira ga 'yan kwamitin akan su gujewa dabi'ar nan ta Copy and Paste ko Forwarding batare sun duba anfani ko rashin amfanin abinda zasu tura ba.
* Anyi kira ga shugabannin Kungiya a dukkan matakai akan rinka tantance wadanda ya kamata su zama shugabannin kwamitin.
* Anyi Kira ga shugabancin kwamitin na kasa akan Su Farfado da Zauren nan na wakilan Kasa da Jihohi.
Zaman taron ya samu halartar dinbin mutane daga wakilan kwamitin a matakin Kasa, Jihohi da kananan hukumomi.
Muna Addu'an Allah ya Bamu ikon sauke nauyin dake kanmu. Allah ya bamu ikon neman yardar Shi da wannan aiki.
Nazeer Mukhtar Danjagale,
Asst. National Secretary II,
Jibwis Social Media Nigeria.
16/Rabi-ul-Awwal/1439
05/December/2017.

No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve