As.Ta Musulunta ya yaudare ta. ya kama mata
gida, yayi mata ciki, ya kaita asibitin shi an zubar
da cikin, ya kaita gidan yari. don Allah ku daure
mu hadu yau 0430pm. As.
Saqon Mal Ashafa Aliyu kenan sakataren
kwamitin musuluntarwa na jihar Katsina.
Daga cikin dalilan da ya sa na so tattaunawa
wannan batu anan shine irin sanin matsalolin da
wannan kwamiti na su Mal Ashafa ya ke
fuskanta. Ba a fi sati guda ba na ga Dan uwa Mal
Sulaiman Yakubu Musa na ga yayi rubutu yana
bayyana halin da masu musuluntar suke tsintar
kansu musamman idan su ka zo yin aure
matsalar kayan daki (gado, katifa dss) wanda
acikin rubutun sa har yana yabon Kwankwaso
kan kokarinsa ta wannan fanni.
Kwamitin Musuluntarwa na Jihar Katsina daddan
kwamiti ne wanda tun lokacin Mariganyi Sarki
Alhaji Kabir Usman Nagogo yake wanda a lokacin
Sarki na Yanzun shine uban wannan kwamiti a
matsayinsa na Magajin gari a wancan lokacin, a
loiacin kwamitin yana samun tallafi na
musamman daga gwamnatin jihar Katsina don in
ban manta ba a lokacin mulkin Mal Umaru Musa
kwamitin ya sa mu gata sosai haka kuma masu
musulunta sun samu gata wanda a lokacin
yawanci masu musulunta suna kalkashin kulawar
matar gwamna Turai Umar don in ban manta ba
har sarauta Kauran Katsina ya bata na
Mujaddadar addinin Musulunci. Haka kuma
Fatima Shema ta gaje ta a wannan taimakon duk
da sukar ta da ake yi cewa ita kirista ce ko ta na
taimakwa yan uwanta kirsitoci amman bata gaza
ba wajan taimakawa masu musuluntar. Duka
Allah ya saka masu da alheri.
In takaice maku magana dai wannan kwamiti da
kuma su kansu wadanda su ka musulunta ko
wadanda za su musulunta nan gaba to suna cikin
halin ko in kula daga gwamnatin jihar Katsina da
kuma masu hannu da shuni na wannan jiha duk
da akwai masu hannu da shunin da har yau har
gobe suna bada gudummuwarsu.(ba wai dole ne
sai gwamnati da masu hanu da shuni sai sun
taimaka, kyautatawa kaine idan sunyi hakan)
Kwanan baya kwamitin ya ziyarci mai girma
Shugaban majalisa Rt. Abubakar Yahya Kusada
wanda muna fatan kudurorin da kwamitin ya isar
gaban sa za a aiwatar ma kwamitin wanda yin
hakan fa yi ma kaine.
Akwai abubuwa da yawa amman zan tsaya anan.
Hassan Kabir Yaradua
14/11/2017

No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve