Monday, 3 April 2017

Kungiyar Izala ta kammala ziyarar jihohi takwas a cikin Naijeriya


Tawagar Kungiyar Izala karkashin jagorancin Sheik Abdullahi Bala Lau ta kammala ziyarar data kai a jihohin Bauchi, Gombe, Adamawa, Taraba, Zamfara, Sokoto, Kebbi da 
Katsina yau lahadi.

Ziyarar wadda tawagar ta zaga jihohin ta kwashe kusan yini biyu a ko wace jiha domin tattaunawa da 'ya'yan kungiyar a dukkan matakai

A halin yanzu tawagar ta tafi hutu na wasu kwanaki, kafin daga bisani ta dawo a ci gaba da kai ziyara zuwa wasu jihohin in Allah ya amince.

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve